Gwamnatin Nijeriya ta yi gargadin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na tsawon kwana biyar wanda zai jawo ambaliyar ruwa a jihohi 19 da ke kasar.
Cibiyar da ke Hasashe da Gargadi kan Ambaliyar Ruwa wacce take karkashin Ma’aikatar Muhalli ta kasar, ta bukaci duka masu ruwa da tsaki kan al’amarin da su fara daukar matakan da suka kamata don tunkarar matsalar.
