| Hausa
An ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo
An ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo
A ranar Jumma'a ne Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana ceto mutanen, bayan sun kwashe makonni a hannun 'yanbindiga, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da kuma zargin gwamnatin Nijeriya na rashin tabbatar da tsaro.

Ɗaya daga cikin malaman da aka sace tare da ɗalibai yayin harin da 'yanbindiga suka kai wa al'ummar Ahoro-Esiele da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu ta bayyana matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da jami'an tsaron Nijeriya bayan an ceto tare da kuɓutar da dukan ɗalibai da malaman.

Da take bayani a madadin sauran waɗanda aka kuɓutar, malamar ta jaddada cewa ba don ƙoƙarin shugaban ƙasa ba da tuni an kashe su.

Ƙarin Bidiyoyi
Makudan kudin fansa da masu garkuwa da mutane ke samu a Nijeriya
Jama'a sun yi dashen shinkafa don nuna rashin amincewa kan jinkirin aikin hanya
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abubuwan da za su iya yin illa ga lafiya
Ko kun san cewa talauci yana rage kaifin basira?
Me ya sa manyan maza suke kuka saboda kwallon kafa?
Me harin Saudiyya da Amurka a Iraki ke nufi?
Me ya sa daukar cikin 'yan mata masu shekaru 15-19 ya zama abin damuwa a Ghana?
Kasar da ake cin tarar wadanda ba su fita kada kuri'a ba
Kasashen Afirka 10 da suka fi yawan mutanen da suka mallaki dala miliyan daya
Matasa kada ku bari a yi amfani da ku a cuci kasarku, in ji Ibrahim Traore