| Hausa
Jirgin ƙarshe ya kwaso 'yan Nijeriya 208 daga Afirka ta Kudu
Afirka
Jirgin ƙarshe ya kwaso 'yan Nijeriya 208 daga Afirka ta Kudu
Rukunin ƙarshe na ’yan Nijeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar hare-haren ƙyamar baƙi ya isa Legas.

An dawo da mutanen ne a cikin jirgin saman Air Peace, wanda ya sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas ranar Laraba.

Tun da farko, gwamnati ta gudanar da jigilar dawo da ’yan Nijeriya sau shida ta jiragen sama, inda ta dawo da ɗaruruwan ’yan Nijeriyar daga Afirka ta Kudu sakamakon yadda ake cikin fargaba saboda hare-haren da suka shafi ƙyamar baƙi.

Ƙarin Bidiyoyi
Ankara da Istanbul: Mene ne bambancinsu?
Makudan kudin fansa da masu garkuwa da mutane ke samu a Nijeriya
Jama'a sun yi dashen shinkafa don nuna rashin amincewa kan jinkirin aikin hanya
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abubuwan da za su iya yin illa ga lafiya
Ko kun san cewa talauci yana rage kaifin basira?
Me ya sa manyan maza suke kuka saboda kwallon kafa?
Me harin Saudiyya da Amurka a Iraki ke nufi?
Me ya sa daukar cikin 'yan mata masu shekaru 15-19 ya zama abin damuwa a Ghana?
Kasar da ake cin tarar wadanda ba su fita kada kuri'a ba
Kasashen Afirka 10 da suka fi yawan mutanen da suka mallaki dala miliyan daya