25 Yuli 2025
Kimanin kwanaki 10 ke nan da rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a wani asibiti mai zaman kansa da ke tsakiyar birnin Landan.
Sai dai batun jinyar tsohon shugaban da rasuwarsa a Landan ya kara fito da mawuyacin halin da ɓangaren kiwon lafiya yake ciki a Nijeriya, inda masu mai fada a ji da masu rike da mukami ba sa iya neman magani a cikin kasar, galibi suna zuwa ne kasashen ketare don neman lafiya.
