| Hausa
Atiku Abubakar ya ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja
00:37
Atiku Abubakar ya ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya kai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyara a gidansa da ke Abuja ranar Laraba, kwanaki kadan bayan Kwankwaso ya shiga Jam'iyyar hamayya ta ADC.
8 awanni baya

Atiku ya ce ya kai ziyarar ne a madadin ADC don rungumar Kwankwaso a yunkurin da suke na kaiwa ga nasara a zabukan 2027.

Kwankwaso ya ce a shirye yake ya yi aiki da duka shugabannin Jam'iyyar ADC a dukkan matakai domin cika burinsu.

Ƙarin Bidiyoyi
Yadda a-daidaita-sahu na 'mata zalla' ke sauya sufuri a birnin Kano
'Yansandan Isra'ila sun far wa yahudawa masu zanga-zangar adawa da hukuncin kisa
Turkawa na murnar sake komawa gasar cin kofin duniya bayan shekara 24
Isra'ilawa sun yi gudun neman mafaka a Haifa
Makami mai linzami na Iran ya sauka a kusa da dakarun Amurka a yankin Gulf
Motoci da yawa sun kone a Isra'ila bayan Iran ta kai hari da bam mai 'ya'ya
TRT Afirka ta cika shekara 3
Nijeriya na fuskantar tsadar fetur duk da matatar Dangote na aiki da cikakken karfin ta
An yi gagarumar zanga-zanga a fadin duniya don adawa da yakin Amurka-Isra'ila a Gabas ta Tsakiya
Yadda dubban mutane suka taru yayin da Kwankwaso ya yi rejistar shiga jam'iyyar ADC