16 Yuli 2025
Wani mutum a ƙasar Iraƙi ya riƙa kaɗa gurmi a yayin da ake yi masa tiyata domin cire wani ƙari a ƙwaƙwalwarsa.
Da yake an yi masa allurar rage raɗaɗi, mutumin ya riƙa taimaka wa likitoci da ke lura da yadda ƙwaƙwalwarsa ke aiki tare da ƙoƙarin kauce wa yin illa ga sassan da ke ba shi damar yin magana da motsi da tunani.
