4 awanni baya
Wannan al’amari yana faruwa ne lokacin da iska mai ƙarfi ta kwaso yashi daga hamadar Sahara inda ta ratsa Bahar Rum. Ƙurar ta mamaye Birnin Heraklion yayin da ake yin guguwa tare da ruwan sama da iska mai ƙarfi, abin da ya haddasa hazo, kuma ya tilasta wa jiragen sama da dama da ke shirin sauka sauya akalarsu zuwa wasu wuraren.
