25 Yuli 2025
Bayanai daga yankin Gaza na Falasɗinu sun nuna yadda dubun dubatar Falasɗinawa suke fama da tsananin gajiya da jigatuwa sakamakon rashin abinci da ruwa. Isra'ila dai tana ci gaba da azabtar da su da yunwa bayan da ta hana shigar da kayan agaji na abinci zuwa yankin da ta yi wa ƙawanya tun da ta ƙaddamar da yaƙin kisan ƙare-dangi a watan Oktoban 2023.
