| Hausa
Iran da Amurka na musayar hare-hare
Iran da Amurka na musayar hare-hare
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta ce ta kai hare-hare a sansanonin Amurka a ƙasashe shida na yankin Larabawa da suka haɗa da Bahrain da Kuwait da Oman da Jordan da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda ta yi wa Amurka mummunar ɓarna.

Iran ta lalata tsarin tsaron sararin samaniya a Oman, sannan ta kai hare-hare a sansanin Sojin Sama na Yarima Hassan Air Base da ke Jordan, da kuma lalata wata cibiyar bayar da umarnin soji da ke Qatar.

A nata ɓangaren, Amurka ta kai hare-hare Iran a kwana na uku a jere bayan Shugaba Trump ya sake bayar da umarnin toshe hanyoyin tashoshin jiragen ruwan Iran tare da ƙaƙaba harajin da ya kai kashi 20 cikin ɗari kan duk wani jirgi da zai wuce.

Ƙarin Bidiyoyi
Makudan kudin fansa da masu garkuwa da mutane ke samu a Nijeriya
Jama'a sun yi dashen shinkafa don nuna rashin amincewa kan jinkirin aikin hanya
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abubuwan da za su iya yin illa ga lafiya
Ko kun san cewa talauci yana rage kaifin basira?
Me ya sa manyan maza suke kuka saboda kwallon kafa?
Me harin Saudiyya da Amurka a Iraki ke nufi?
Me ya sa daukar cikin 'yan mata masu shekaru 15-19 ya zama abin damuwa a Ghana?
Kasar da ake cin tarar wadanda ba su fita kada kuri'a ba
Kasashen Afirka 10 da suka fi yawan mutanen da suka mallaki dala miliyan daya
Matasa kada ku bari a yi amfani da ku a cuci kasarku, in ji Ibrahim Traore