| Hausa
'Yanwasan Iran na atisaye a Turkiyya gabanin wasansu da Nijeriya
00:54
'Yanwasan Iran na atisaye a Turkiyya gabanin wasansu da Nijeriya
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran ta gudanar da atisaye a kudancin Turkiyya a ranar Laraba 25 ga Maris, yayin da take shirye-shiryen tafiya gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Amurka ta Arewa.
26 Maris 2026

Ana sa ran tawagar za ta ja hankali sosai a wannan karon, sakamakon yanayin yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.

Tawagar ta gudanar da atisayen ne a Belek, wani yankin shaƙatawa kusa da birnin Antalya da ke gaɓar tekun Medatareniya.

An takaita damar manema labarai sosai, inda jami'ai suka bayyana cewa suna son kauce wa duk wani abin da zai janye hankalin 'yanƙwallon kafin wasannin share fage masu zuwa, waɗanda aka bayyana a matsayin masu muhimmanci ga shirye-shiryensu.

A ƙarshen wannan mako Iran za ta buga wasanni biyu a Antalya, tsakaninta da Nijeriya da kuma Costa Rica. Jami'an tawagar sun bayyana cewa waɗannan wasannin jigo ne ga shirye-shiryensu na ƙarshe.

Asali an shirya gudanar da wasannin na sada zumunci ne a ƙasar Jordan, amma aka mayar da su Turkiyya biyo bayan ɓarkewar yaƙin Iran.

Ƙarin Bidiyoyi
Taron ƙasa da ƙasa kan dabarun watsa labarai 'Starcom Summit'
An yi mamakon ruwan sama a masallacin ka'aba
''An rusa gaba daya sansanonin Amurka a yankin''
Sharhi kan sharudda biyar da Iran ta gindaya kafin tsagaita wuta
Masu bayar da agaji sun ciro wani uba da 'dansa daga kasan baraguzai
Mamakon ruwan sama ya lalata hanyoyi da motoci a arewancin Oman
Akalla mutum 24 sun mutu bayan motar Bas ta fada kogi a Bangladesh
Yadda wasu mata Musulmai da Kiristoci ke tsare unguwanninsu a jos
'Yansanda sun gano wajen buga kudin Euro na jabu a iyakar Romania da Bulgaria
Barna da hare-haren Amurka da Isra'ila suka yi a kasuwar Isfahan ta Iran