Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gargadi Tel Aviv kan yadda za ta dandana kudarta dangane da wasu rahotanni da ke cewa Isra'ilar na shirin kashe mambobin Hamas wadanda ke rayuwa a wajen Falasdinu.
"Idan suka kuskura suka dauki wannan matakin kan Turkiyya da mutanenta, za su girbi abin da suka shuka ta yadda ba za su iya farfadowa," kamar yadda Erdogan ya shaida wa 'yan jarida a ranar Lahadi a lokacin da yake cikin jirgin dawowa daga Qatar bayan an tambaye shi dangane da wani rubutu da aka yi kan mujallar Wall Street da ke cewa akwai shirin kashe mambobin Hamas din da ke rayuwa a wajen Falasdinu.
"Wadanda suka yi yunkurin yin hakan kada su manta da abin da zai biyo baya yana da tsanani. Babu wanda bai san Turkiyya kan ci gaba wurin leken asiri da kuma ayyukan tsaro a waje. Haka kuma mu kasarmu ba sabuwa bace," in ji shi.
Gargadin na Erdogan na zuwa ne bayan Ronen Bar, shugaban hukumar Shin Bet na Isra'ila ya bayyana cewa Isra'ila ta fitar da tsare-tsare domin kashe mambobin Hamas da ke wajen kasar.
“A duk wani wuri da ke Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan da Lebanon da cikin Turkiyya da Qatar, ko ina,” kamar yadda Bar ya bayyana a wani sakon murya. “Hakan zai dauki tsawon shekaru amma za mu iya gudanar da hakan.”
Gaza ta Falasdinawa ce
Gaza ta Falasdinawa ce kuma Falasdinawan ne za su yanke hukunci kan wadanda za su jagorance ta, kamar yadda Erdogan ya bayyana a lokacin da yake Allah wadai da shirin da Isra'ila ke yi na samar tudun mun tsira a Gaza mai tsawon kilomita 40 da fadin kilomita 12.
"Abin da ya fi kamata Isra'ila ta yi shi ne kafa kasar Falasdinawa mai zaman kanta kan iyakar da aka shata ta 1967 da kuma mayar da yankunan Falasdinawa da aka mamaye ga masu su," in ji Erdogan.
Yayin da yake nuna muhimmancin sake gina Gaza, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa "za mu kara karfafa tattaunawarmu da kasashen yankin Gulf domin cimma burin warkar da ciwon da ke tattare da 'yan uwanmu maza da mata Falasdinawa da kuma kafar kasar Falasdinu dangane da iyakar 1967 da aka shata."