Logo
    • Türkiye

      Türkiye

    • Afirka

      Afirka

    • Duniya

      Duniya

    Labarai

    • Kasuwanci

      • Wasanni

        • Ra’ayi

          • Rayuwa

            • Bidiyo

              • Karin Haske

                  • English

                    English

                  • Français

                    Français

                  • Swahili

                    Swahili

                  Hausa


                Bidiyoyin da ke shafukan sada zumunta

                Kantin Kwari: Kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka Kantin Kwari: Kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka

                Kantin Kwari: Kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka

                Kasuwar Kantin Kwari da ke birnin Kano na Arewacin Nijeriya, wadda aka kafa a shekarun 1930, ita ce kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka, inda take taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin yankin. Dubban mutane daga ciki da wajen Nijeriya suna zuwa kasuwar domin gudanar da harkokin kasuwanci, kamar yadda za ku gani a wannan rahoto na musamman da Yusuf Ibrahim Yakasai ya haɗa mana, yayin da ya ziyarci kasuwa.
                Boko Haram: Halin da ‘yan gudun hijirar Nijeriya suke ciki a ƙasar Chadi Boko Haram: Halin da ‘yan gudun hijirar Nijeriya suke ciki a ƙasar Chadi

                Boko Haram: Halin da ‘yan gudun hijirar Nijeriya suke ciki a ƙasar Chadi

                Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar Nijeriya da ke Chadi sun shaida wa TRT Afrika Hausa irin mummunan halin da suka shiga bayan mayaƙan Boko Haram sun tilasta musu yin hijira.Sun bayyana cewa akwai lokacin da suka taɓa shafe watanni 11 ba su samu tallafin ko da kwano ɗaya na abinci ba.
                Lugude: Mutumin da ke wallafa tsofaffin hotunan arewacin Nijeriya Lugude: Mutumin da ke wallafa tsofaffin hotunan arewacin Nijeriya

                Lugude: Mutumin da ke wallafa tsofaffin hotunan arewacin Nijeriya

                Daya daga fitattun masu wallafa tsofaffin hotunan tarihi na Nijeriya musamman ma na arewa a shafukan sada zumunta Buhari Sale Abubakar, da aka fi sani da Lugude ya bayyana in da yake samun hotunan da yake wallafawa da hotunan da suka fi jan hankalin masu bin shafinsa.
                Zan iya auren mace irin Samira ta shirin Garwashi Zan iya auren mace irin Samira ta shirin Garwashi

                Zan iya auren mace irin Samira ta shirin Garwashi

                Fitaccen ɗan wasan Kannywood Yakubu Muhammad ya yi ƙarin bayani dangane da irin rawar da yake takawa a cikin wasu fina-finai masu dogon zango da yake ciki waɗanda suka haɗa da Garwashi da Labarina da Gidan Sarauta
                Ba na so na samu matsala a Kannywood har lokacin da zan yi aure - Ma'u ta Fim ɗin Garwashi Ba na so na samu matsala a Kannywood har lokacin da zan yi aure - Ma'u ta Fim ɗin Garwashi

                Ba na so na samu matsala a Kannywood har lokacin da zan yi aure - Ma'u ta Fim ɗin Garwashi

                ‘Yar wasan Kannywood ɗin nan wadda tauraruwarta ke haskawa Nana Fiddausi Yahaya wadda aka fi sani da Asmau a shiri mai dogon zango na Garwashi ta shaida wa TRT Afrika Hausa yadda ta tsinci kanta a harkar fim da kuma wasu nasarori da ta samu.
                Ni ‘yar Nijar ce amma ina alfahari da Nijeriya – Fati Nijar Ni ‘yar Nijar ce amma ina alfahari da Nijeriya – Fati Nijar

                Ni ‘yar Nijar ce amma ina alfahari da Nijeriya – Fati Nijar

                Shahararriyar mawaƙiyar nan ta Kannywood, Binta Labaran wadda aka sani da Fati Nijar ta ce 'yan'uwantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Nijar da Nijeriya ce ta sanya ta rera waƙa a kan ƙasashen biyu. A hirar da ta yi da TRT Afrika Hausa, Fati Nijar ta bayyana sirrin ɗaukakarta da kuma daɗewarta a fagen waƙa.
                Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya

                Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya

                Kasuwar sayar da kwaɗi da ke Jihar Kano na daga cikin kasuwannin da suka shahara wurin sayar da kwaɗi a Nijeriya. Sakamakon yadda kasuwancin kwaɗi ke bunƙasa, masu sana’ar a kasuwar kwaɗi ta Na’ibawa na biyan haraji ga gwamnati kamar sauran ‘yan kasuwa kuma gwamnatin na amfani da kuɗaɗen wurin aiwatar da ayyukan more rayuwa.
                Hanyar Abuja-Kaduna: Lalacewar hanya mafi muhimmanci a arewacin Nijeriya Hanyar Abuja-Kaduna: Lalacewar hanya mafi muhimmanci a arewacin Nijeriya

                Hanyar Abuja-Kaduna: Lalacewar hanya mafi muhimmanci a arewacin Nijeriya

                Hanyar Abuja zuwa Kaduna hanya ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya inda dubban motoci ke bin hanyar a kullum. Ana yawan samun hatsarin mota a hanyar da cunkoson ababen hawa sakamakon yadda hanyar ta lalace duk da cewa an shafe tsawon shekaru ana gyaran hanyar amma ba a kammala ba. 
                Logo
                Hakkin mallakar TRT Afirka 2025

                Ma’aikata

                • Game da TRT Afirka
                • Tuntube Mu

                Dokoki

                • Ka’idoji Tsare Sirri
                • Ka’idojin Amfani da Cookie
                • Ka’idoji da Sharuddan Amfani
                • TRT Afirka Youtube
                • TRT Afirka Twitter
                • TRT Afirka Facebook
                • TRT Afirka Instagram
                • TRT Afirka TikTok