1335 GMT — Kasashen G-7 sun goyi bayan sake tsagaita wuta a Gaza
Kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya ta (G-7) ta goyi bayan sake tsagaita wuta a yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa bayan taron ƙolin da suka yi da yammacin jiya Laraba, ƙasashen G-7 sun ce: "Mun kuma damu matuƙa da mummunan halin da fararen hular Falasdinawa ke ciki a Gaza."
Da suke kira da a dauki matakin gaggawa don magance taɓarɓarewar rikicin jinƙai, shugabannin G-7 sun ce: "Dole ne kuma a dauki ƙwararan matakai don hana gudun hijirar karin mutane da kuma kare kayayyakin more rayuwa na farar hula."
1338 GMT — Adadin Falasdinawan da suka mutu a Gaza ya haura 17,000
Hukumomi a Gaza sun ce adadin Falasdinawa baki daya ya ƙaru zuwa 17,177 tun bayan fara yaƙin Isra'ila a yankin.
Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 350 tare da jikkata 900 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Ma'aikatar ta kara da cewa kawo yanzu kusan mutum 46,000 ne suka jikkata
1200 GMT — Tankar yaƙin Isra'ila ta kashe dan jaridar Reuters a Lebanon
An yi amfani da tankokin yaƙi guda biyu na Isra'ila a harin da ya kashe ɗan jaridar kamfanin dillancin labarai na Reuters tare da raunata wasu mutum shida a kudancin Lebanon a ranar 13 ga watan Oktoba, kamar yadda wani bincike da kamfanin dillancin labaran ya wallafa ya gano.
Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya gudanar tare da Airwars, wata kungiya mai zaman kanta da ke gudanar da bincike kan hare-haren da ake kai wa fararen hula a cikin yanayi na rikici, ya nuna cewa harin na farko ya hada da harsashin tanki mai tsawon milimita 120 da sojojin Isra'ila kawai suke amfani da su a wannan yanki.
Amnesty da Human Rights Watch sun kuma ce harin na farko da ya kashe ɗan jaridar Reuters Issam Abdallah tare da raunata mai ɗaukar hoto na AFP Christina Assi mai yiwuwa wata tanka ce da aka harba daga Isra'ila.
1042 GMT — Duka asibitocin arewacin Gaza sun daina aiki - Ma'aikatar Lafiya

Dukkan asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki a halin yanzu, duk kuwa da ƙoƙarin da ake yi na ganin an farfaɗo da dukkan asibitocin da hare-haren Isra'ila suka lalata su.
A wata sanarwa, mai magana da yawun Ma'aikatar Lafiya ta Gaza Ashraf al Qudra, ya ce tawagogin lafiya na fuskantar matsaloli a ƙoƙarinsu na aiki a Asibitin Al Shifa da ke yammacin Gaza - wanda shi ne asibiti mafi girma a Gaza.
"Za mu ci gaba da ƙoƙrinmu na ganin an samu asibirtin da ke aiki a Zirin Gaza duk da matsalolin da muke fuskanta," in ji al Qudra.
Al Qudra ya ce Asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza ya cika maƙil da kusan mutum 1,000 da suka ji raunuka, inda marasa lafiya ke kwakkwance a ƙasa.
Ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya kuma ambato Maher Shamiyya, wani jami'in ma'aikatar yana cewa babu lantarki a Al Shifa kuma ya cika maƙil da mutanen da ke neman mafaka.
0531 GMT — Kotun ICC ta ce hana shigar da agaji Gaza zai iya zama laifin yaki
Babban Mai Shigar da Kara na Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) Karim Khan ya yi kakkausan gargadi cewa hana shigar da kayan agaji ga fararen-hula yankin Gaza zai iya zama laifin yaki.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na intanet, Khan ya yi magana kan wasikar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya aika wa Kwamitin Tsaro (UNSC), inda zai yi amfani da Ikon da Sashe na 99 ya ba shi da zai iya kai agaji na tura agaji Gaza ba tare da shamaki ba domin hana barkewar babban bala'i da kuma wanzar da zaman lafiya a duniya.
Khan ya jaddada muhimmancin bari a kai kayan agaji Gaza, yana mai bayyana cewa hana kai wasu kaya yankin ga fararen-hula da gangan tamkar laifin yaki ne a Yarjejeniyar Rome ta ICC.
"Ina jaddadawa karara cewa hana shigar da kayan agaji ga fararen-hula yana iya zama laifin yaki a tsarin Yarjejeniyar Rome ta ICC," in ji Khan.
0230 GMT — Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a kudancin Gaza yayin da Isra'ila ta mamaye yankin
Mayakan gwagwarmayar Hamas sun gwabza da sojojin mamaya na Isra'ila a tsakiyar babban birnin Gaza na kudancin kasar inda Isra'ila ke kyautata zaton akwai babban jagoran Hamas, yayin da Isra'ila ta matsa ƙaimi a yankin da ta yi wa ƙawanya.
Shaidu sun ce sojojin Isra'ila da tankunan yaƙi masu sulke da kuma manyan motocin yaƙi sun yi ta kai kawo a cikin Khan Yunus, lamarin da ya tilasta wa fararen hula da suka rasa matsugunansu sake tserewa, in ji shaidu.
Kungiyar Hamas ta ce da yammacin jiya Laraba a kafar Telegram cewa mayakanta na ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa da sojojin da suka mamaye "dukkan yankuna suna kutsawa cikin Zirin Gaza", kamar yadda ta yi ikirarin cewa sun lalata motocin sojin Isra'ila biyu a Khan Yunis da Beit Lahia a arewacin yankin.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo ya ce sojojin Isra'ila suna kutsawa gidan shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar, inda mai magana da yawun Netanyahu ya ce Sinwar din na wani ginin karkashin kasa a yankin Khan Yunis.
Sai dai kungiyoyin agaji sun yi gargadin yaduwar yaƙin da Isra'ila ke yi a kudancin Zirin Gaza zai sa fararen hulan da suka tsere daga arewacin kasar, wadanda a yanzu yawancinsu sun shiga halin ha'u'la'i da rashin zaɓin inda za su.
"Muna cikin ɓacin rai, mun kai maƙura," in ji Amal Mahdi mazauniyar Khan Yunis. "Muna bukatar wanda zai nemo mana mafita domin mu fita daga cikin wannan hali."

2210 GMT — Isra'ila ta ce wa'adin mulkin Antonio Guterres "haɗari ne ga zaman lafiyar duniya"
Ministan Harkokin Wajen Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Eli Cohen ya ce wa'adin shugaban Majalisar Dinkin Duniya hatsari ne ga zaman lafiyar duniya, yana mai cewa kiran da ya yi na tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila ke yi da Gaza da aka yi wa ƙawanya ya zama "goyon baya ga Hamas".
"Bukatarsa [Antonio Guterres] ta amfani da shafi na 99 da kuma kiran tsagaita wuta a Gaza ya ƙunshi goyon bayan ƙungiyar ta'addanci ta Hamas da kuma amincewa da kisan tsofaffi, da sace jarirai da fyaɗe ga mata," in ji Cohen, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.
Ya ƙara da cewa "duk wanda ke goyon bayan zaman lafiya a duniya dole ne ya goyi bayan ƙwato yankin Gaza daga hannun Hamas."