Wakilai da lauyoyin kungiyoyin kwadagon ba su halarci zaman kotun ba. Hoto/OTHER

Wata Kotun Ma'aikata da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta umarci kungiyoyin kwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC) su dakatar da yajin aikin da suke shirin gudanarwa sakamakon janye tallafin man fetur.

Alkaliyar kotun, Olufunke Anuwe ce ta bayar da wannan umarni ranar Litinin bayan gwamnatin kasar ta gabatar mata da bukatar hakan.

Wakilai da lauyoyin kungiyoyin kwadagon ba su halarci zaman kotun ba.

Alkaliyar ta hana kungiyoyin kwadagon shiga yajin aikin da suka dauki aniyar somawa ranar Laraba 7 ga watan Yuni.

Da take bayani game da bukatar da Maimuna Shiru ta ma'aikatar Shari'ar kasar ta gabatar mata, alkaliya Anuwe, ta amince cewa yajin aikin zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar sannan ya jefa 'yan Nijeriya a mawuyacin hali.

Kazalika alkaliyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta mika wa kungiyoyin kwadagon hukuncin da ta yanke.

Daga nan ta dage zaman sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Yuni.

Gabanin hukuncin kotun, gwamnatin Nijeriya ta ce za ta yi nazari kan bukatun da kungiyar kwadago ta kasar ta gabatar mata da zummar hana ta tafiya yajin aikin.

Daga cikin bukatun akwai kara mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N200,000 da samar da motocin sufuri na gwamnati ga kowanne dan kasa.

Ma'aikatan Lafiya sun janye daga shiga yajin aiki

Tun da farko, Ma'aikatan lafiya na Nijeriya sun sanar da janye yajin aikinsu na kwanaki 12 bayan sun gana da shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.

Kungiyar ma'aikatan Lafiya, JOHESU, ta ce ta janye yajin aikin ne saboda ta bai wa gwamnati wa'adin mako uku don magance matsalolin da suke fuskanta.

TRT Afrika