“Bashin da muka biya na kuɗin ƙasashen waje ya bai wa masu zuba jari da ƴan kasuwa da sauran abokanmu ƙarfin gwiwa, abin da ya sa suka ƙara hada-hada a kasuwar musayar kuɗi ta Nijeriya,” in ji Cardodo.  / Hoto: Reuters

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Yemi Cardoso ya ce matakan da suka ɗauka na biyan bashin dalolin da ake bin su sun sa naira ta kasance kuɗin da ya fi samun tagomashi a duniya a yanzu haka.

Cardoso ya bayyana haka ne ranar Asabar bayan kammala taron da Bankin Duniya da Asusun Bayar da Lamuni na IMF suka gudanar a birnin Washington DC na Amurka.

A watannin baya bayan nan darajar kuɗin Nijeriya ta yi matuƙar karyewa idan aka kwatanta da dalar Amurka lamarin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki da kuma ƙara tsadar rayuwa a tsakanin ƴan ƙasar.

Sai dai matakan da CBN ya ɗauka ciki har da biyan bashin dala biliyan bakwai da ake bin sa da kuma yin garambawul a kasuwar canji sun taimaka wurin farfaɗowar darajar naira.

“Naira ta kasance kuɗin da ya fi samun tagomashi a duniya a watan Afrilu... kasuwarmu ta kuɗaɗen waje tana samun babban tagomashi inda ta samu darajar da ba a taɓa ganin irin ta ba a cikin shekaru bakwai,” in ji shi.

“Bashin da muka biya na kuɗin ƙasashen waje ya bai wa masu zuba jari da ƴan kasuwa da sauran abokanmu ƙarfin gwiwa, abin da ya sa suka ƙara hada-hada a kasuwar musayar kuɗi ta Nijeriya,” a cewar Cardoso.

Sai dai Gwamnan CBN ya ce ba za su saki jiki ba domin suna sane da irin ƙalubalen da tattalin arzikin Nijeriya yake fuskanci ciki har da ƙarin hauhawar farashi.

TRT Afrika da abokan hulda