Shugaba Ramaphosa  ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin firaministan Singapore Lee Hsien Loong. Hoto/Reuters

Shugabannin kasashe shida daga Afirka za su tafi Ukraine da Rasha "nan ba da jimawa ba" domin yunkurin sulhunta kasashen da ke yaki da juna, kamar yadda shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana ranar Talata.

Bai fadi ranar da za su tafi ba ko kuma cikakken bayani game da balaguron wanda shugabannin kasashen Zambia, Senegal, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Uganda, Masar da Afirka ta Kudu da za su yi ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin firaiministan Singapore Lee Hsien Loong.

Cyril Ramaphosa ya ce shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky sun yi maraba da yunkurin shugabannin Afirka, kuma "sun yarda mu tarbe mu a Moscow da Kyiv."

Ramaphosa ya ce ya tattauna "ta wayar tarho" da Shugaba Putin da Zelensky game da batun a karshen makon jiya.

"Babban dalilinmu na son zuwa kasashen shi ne mu tattauna kan yunkurin samun zaman lafiya domin kawo karshen mummunan rikicin Ukraine, wanda yake haddasa mutuwar jama'a sannan yake tasiri ga kasashen Afrika," in ji shi.

Shugaba Ramaphosa ya ce sun sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Kungiyar Tarayyar Afirka game da wannan yunkurin kuma dukkansu sun yi maraba da hakan.

TRT Afrika da abokan hulda