'Yan gudun hijirar Sudan da ke gujewa yaƙi a Darfur suna isa kusa da iyaka tsakanin Sudan da Chad a garin Goungour ranar 8 ga Mayu, 2023. / Hoto: Reuters

Daga Yassmin Abdel- Magied

Kwanaki kaɗan kafin shiga shekara ta biyu da fara yaƙin basasan Sudan, an fara tararrabin barazanar wani rikicin a el-Fasher, da ke Darfur.

Yayin da ake ɗari-ɗarin birnin zai zama sabon fagen daga, manyan jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargaɗin cewa sama da farar-hula 800,000 suna cikin "matsanancin haɗari," baya ga tarin alamun faruwar farmaki, haɗi da ƙona ƙauyukan da ke kusa.

Aƙalla 'yan gudun hijira rabin miliyan da waɗanda yaƙi ya tagayyara ne da a yanzu suke samun mafaka a babban birnin Arewacin Darfur, suke fargaba kan rayuwarsu, ga shi ba inda za su gudu.

Masana sun ce damar da ake da ita ta tsayar da kisan gillar da ke shirin faruwa tana gushewa cikin sauri. A cewar Nathaniel Raymond, daraktan gudanarwa na Cibiyar Bincike kan Jinƙai ta Jami'ar Yale, haɗarin ya kai "matakin harin Hiroshima da Nagasaki."

Da yake jawabi a taron manema labarai, ya ce, "Muna kiran wannan yanayi da ‘makasa.'" Wannan ne yaƙin ƙarshe na Darfur, kuma rundunar RSF tana niyyar "kammala kisan ƙare-dangi da ta fara a 2004/2005," in ji Raymond.

Idanu sun rufe

Makasar da za ta kai mataki irin wanda aka gani a harin nukiliya na Hiroshima da Nagasaki. Rayukan kusan mutane miliyan guda ne ke cikin haɗarin kisan kiyashi. Wannan kalamai suna da wahalar fahimta, kuma suna da rikitarwa. Amma kuma, kisan ƙare dangin na ƙaratowa a Darfur, amma ga shi duniya ta yi biris.

Rundunar RSF tana dab da ƙaddamar da wani zagayen hari, kamar yadda ƙungiyar ta aiwatar lokaci bayan lokaci. Amma kuma ba abin da wannan barazanar ta haifar face 'yan kalamai ga 'yan jarida da ke "kiran a tsagaita wuta." Wannan bai ma kai a ce ka zo yaƙin bindiga da wuƙa ba, sai dai a ce ka zo yaƙin da takarda.

"Yana da matuƙar ciwo ka ga matakin biris da ƙasashen duniya ke nunawa ga Sudan," cewar Hala al-Karib, daraktan yanki na ƙungiyar kishin mata bisa turbar kishin Afirka ta SIHA.

Kalamanta nata sun yi nuni da damuwar al'ummar Sudan a duniya. Zamowa ɗan Sudan ya zamo tamkar mutum yana miƙa ƙoƙon bara don a saurare shi, amma sai a yi watsi da shi a maishe shi hashtag, idan an yi sa'a kenan.

Rikicin da ya kai tsawon shekara guda yanzu, tuni ya samu laƙabin "Yaƙin da Aka Manta" a wajen manyan kamfanonin jarida da kuma masu saka-ido.

Ta yaya aka yi watsi da mu a tarihi, har ake magana da mu a matsayin abin da ya wuce, bayan kuwa yaƙin nan yana raye, yana ƙazamin numfashi?

Gaza tara kuɗi

A halin yanzu Sudan tana zaman mafi munin matsalar jinƙai a duniyarmu, amma an kasa tara kuɗin ciyar da miliyoyin mutane don kaucewa yunwa.

A wani taro a birnin Paris a wannan watan daidai da cika shekara guda da soma yaƙin, masu ba da tallafi daga faɗin duniya sun yi alƙawarin ba da dala biliyan biyu na agaji.

Kamar yadda mai sharhin siyasa Kholood Khair ya yi nuni, yawancin wannan ya haɗa da sauran alƙawuran baya da ba a cika su ba. Duk da haka, "da ba don taron Paris ba da ba wani sabon yunƙuri kan tara kuɗi ga Sudan gabaɗaya," in ji Khair.

Taron ya samu ambato sau ɗaya, ko wataƙila sau biyu a gidajen labarai, amma bayan nan, makomar rikicin Sudan ta kuma komawa abar mantawa.

Akwai tarin dalilai da ya sa yaƙin ba ya samun kulawa a duniya duk da kasancewarsa mummuna; amma kuma, ba na sha'awar zayyana su a nan.

Lokacin yin wannan fashin-baƙi—don bincika me ya sa hakan ke faruwa—ba yanzu ba ne. Wannan tattaunawar ɓata lokaci ce kawai, wadda za ta ɗauke hankali daga buƙatar gaggawar da ke gabanmu.

Wajibe a ɗauki mataki. Babu wani saƙo daga 'yan Sudan da ke can. Dole a ɗauki mataki a duka ɓangarori, ko a samu asarar ɗaruruwa da dubban mutane—ko ma miliyoyi—na rayukan 'yan Sudan farar hula a hannunmu.

Ba za mu ce ba a gargaɗe mu ba. Ko da mutane sun samu hanyoyin tsira da rayukansu - kuma za su yi, saboda al'ummar Sudan haziƙai ne, jajirtattu, masu ƙarfin hali - don haka su ma al'ummar duniya sai su yi nasu ƙoƙarin.

Yin magiya ga mutanen da ke ɗauke da makamai masu niyya aikata kashe-kashe ba tasirin da zai yi. Dabaru, da neman haƙƙi da hukuntawa su ne hanyoyin da za a duba.

Shirin ɗaukar mataki

Me za a iya yi? A nan kusa, akwai kiraye-kiraye kan Amurka ta shirya taron kwamitin tsaro na MDD don a nemi ƙudurin sanya takunkumi kan masu bai wa RSF makamai da kuɗaɗe.

Wajibi a saka matsin lamba kan ƙawayen RSF don su daina samar mata da makamai, saboda ba za ta iya ci gaba da yaƙin ba idan babu tallafin wasu ƙasashen duniya.

Na biyu shi ne magance matsalar yunwa da ke tunkarowa tare da ƙazancewar matsalar jinƙai, gami da ɓarkewar tarin-fuka da sauran cututtuka masu yaɗuwa a sansanonin 'yan gudun hijira a ƙasar.

Matan Sudan suna zanga-zanga kan sojoji a titunan birnin Khartoum, ranar 6 ga Janairu, 2022 (AFP).

Dole a saka matsin lamba kan ɓangarorin da ke yaƙar juna don su bar kayayyakin jinƙai su isa yankuna da ake buƙata, don kaucewa ƙaruwar mace-mace saboda yunwa.

Baya ga kayayyakin jinƙai, wajibi ne a samar da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin bayar da agaji na (ERRs) a faɗin ƙasar, don su samar da abinci ga dubban mutane farar-hula da ke jiran ƙarshen yaƙin.

Tsagaita wuta na dindindin, da sake gina ƙasar, da tsaron al'umma. Tabbatar da alƙawarin Juyin Juya-halin Disamba, gami da kafa gwamnatin farar-hula, da mayar da sojoji bariki. Waɗannnan su ne manyan muradun.

Amma duba da duk abubuwan da muka sani, waɗannan manyan buruka suna da wuyar cimmawa, tamkar bakan gizo ne mai nisa.

Mafarkin zai iya zamowa gaskiya. Da farko dai, bari mu fara yin duk abin da za mu iya wajen hana ƙarin salwantar rayukan al'ummar Sudan.

TRT Afrika