Bankin Musulunci na Raya Ƙasa (IsDB) ya amince da bai wa ƙasashe huɗu dala miliyan 418 don ayyukan cigaba.  / Photo: AA

Bankin Musulunci na Raya Ci gaban Tattalin Arziƙi (IsDB) ya amince da bayar da dala miliyan 418 domin ayyukan ci gaba a Tajikistan da Benin, Ivory coast da Turkiyya.

Kwamitin zartarwa na bankin ya sahale da aiwatar da ayyukan huɗu yayin taronsa karo na 355 l, wanda ya mayar da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

Bankin ya sanar a taronsa na shekara-shekara, wanda ya zo daidai da cikarsa shekaru 50, a babban birnin Saudiyya, Riyadh.

Tajikistan za ta samu dala miliyan 150 don gina tashar lantarki ta Rogun Lot-4, don samar da makamashin lantarki mai tsafta da ƙasar za ta iya dogara a kai.

Benin za ta samu Euro miliyan 60.6 (dala miliyan 65) don ci gaban harkar noman rogo, wanda zai haɓaka wadatar abinci da samar da kuɗaɗe ga al'ummar ƙasar.

Shirin zai kuma inganta tattalin arziƙi da ƙarfin sarrafa kayan noma, da shigowar fannin kamfanoni masu zaman kansu a harkar sarrafa rogo, dankali, da doya.

Ivory coast za ta samu Euro miliyan 70.56 (dala miliyan 75.5) na kuɗaɗe don haɓaka fannin noman rogo, don wadatar da ƙasa da abinci, da ɗaukaka tattalin arziƙi da samar da kuɗin shiga ga mutane ta hanyar noman rogo, da sarrafa shi da haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu.

Kwamitin ya amince da Euro miliyan 120 (dala miliyan 128.5) ga Turkiyya don aikin babban titin Nakkas-Basaksehir, wanda zai kasance wani yanki na babban titin Arewacin Marmara ƙarƙashin shirin gwamnatin ƙasar.

Bankin ya ce game da aikin ci gaba a Turkiyya, "Babbar manufar aikin shi ne samar da wata mashiga, ƙari kan titin tsallaka Bosphorus, don rage yawan ababen hawa da tsaiko, da rage lokacin tafiya, da yawan fitar da iskar gas mai gurɓata muhalli".

TRT Afrika