Sembene ya zama masamar ilhama da zaburar da ‘yan Afirka da dama ta hanyar ayyukansa. Hoto: Others

Daga Awa Cheikh Faye

An san Ousmane Sembene wajen jajircewa da tsayin daka kan batutuwa na siyasa da zamantakewa a cikin ayyukansa na adabi da fina-finai.

Shekaru 16 kenan da rasuwar mutumin da ake wa kallon daya daga cikin kwararrun shirya fina-finai a Afirka.

Ousmane Sembene marubuci, darakta, jarumi kuma marubucin fina-finai da wasanni ne, kuma muhimmi a Afirka a yau, wanda aka haifa a 1923 a Senegal. Ya rasu a ranar 9 ga Yuni, 2007.

Duba da yadda ya yi ayyuka a bangaren adabi, Sembene ya shiga harkokin shirya fina-finai a makare, kuma ya yi amfani da hikimarsa wajen inganta Afirka bayan ‘yan mulkin mallaka da kuma yaki da nuna wariyar launin fata.

Fina-finansa a yanzu sun zama wajen samun ilhama da zaburarwa ga masu shirya fina-finai a Afirka da yawa.

Marubucin fina-finan Tanzaniam darakta kuma mai shirya fina-finai Amil Shivji ya ghadu da ayyukan Sembene lokacin yana jami’a.

Shekaru 16 kenan da rasuwar mutumin da ake wa kallon daya daga cikin kwararrun shirya fina-finai a Afirka. Hoto: Others

Shivji ya fada wa TRT Afika cewa “Abun da na gani shi ne al’adata, al’ummata da salon rayuwa da na gano yana da kusanci da ni.”

Hanyar samun ilimi

Ya kara da cewa “A lokacin da na gano alfanun fina-finansa, sai na fara bibiyar ayyukansa, na nazarci fina-finai wanda suke takaice gwagwarmaya, farin ciki da tsoron jama’ar Afirka da sana’o’insu.”

Sembene ya zama masamar ilhama da zaburar da ‘yan Afirka da dama ta hanyar ayyukansa.

“Na san cewar tabbas zan bibiyi wannan hanya tare da bayar da labarai na gaskiya game da al’ummun da ake nunawa wariya a nahiyar Afirka, musamman a Tanzania,” in ji daraktan fina-finan Tanzania.

Mai shirya fina-finai da kuzari, Ousman Sembene bai taba daina nuna adawa da rashin adalci a yanayin zamantakewa a fina-finai da rubun adabinsa ba.

Mai shirya fina-finai Amil Shivji ya yi bayani kan Sembene da cewa an san shi saboda yawo a yake tare da nuna fina-finai a fadin kasar inda yake tabbatar da kowanne kauye ya samu damar kalla.

Shivji ya ce “Ya tabbatar da cewa ya isa ga jama’ar da suka kamata su kalli fina-finansa.

"A waje na, tunatarwa ce kan wadanne irin labarai ya kamata mu dinga bayarwa game da nahiyar, su wa ya kamata mu fadawa, sannan mu tunawa kanmu cewa damarmu na hannunmu.”

Dan kishin Afirka

Ayyukan daraktan dan kasar Sanagal na bayyana Afirka sama da yadda ake tunani.

“Abun da muke kira ayyuka masu tasiri a yau, shi ne abun da yake yi a shekarun 1960,” in ji Shivji. Fim din san a farko La noire de, da aka yi a 1960, ya lashe kambon Prix Jean Vigo.

Ousmane Sembene ya tafi ya bar ayyuka d asuka hada da gomman kagaggun labarai da zube tare da fina-finai 15. Hoto: Others

A wata tattaunawa da ‘yan jaridu bayan samun wannan kambi, Ousmane Sembene ya ce yana shirya fina-finai.

“Don Magana da mutane ba a cikin kaars akawai ba, har ma da a wasu kasashen, a tattauna matsaloli da suka shafe mu baki daya.

"Matsalolin dukkan kasashe masu tasowa, matsalolin da aka fuskanta a baya, na yanzu da wadanda za a fuskanta a nan gaba.”

Sembene ya rubuta litattafai da dama da ma gajerun labarai, da suka hada da Le Docker noir, wanda kwarewar sa a lokacin yana matsayin dan dako a Marseille.

Les Bouts de bois de Dieu da aka buga a 1960, ya bayar da labari game da ma’aikatan jirgin kasa da ke yajin aiki a tsakanin Dakar da Bamako daga shekarar 1947 zuwa 1948.

Tona asirin Faransa

Wannan ya biyo bayan Le Mandat a 1968, wand aya lashe kambin kasa da kasa a bukin nuna fina-finai na wannan shekarar.

Ya kuma shirya Camp Thiaroye, fim ne game da kisan kiyashi kan ‘yan Tirailleur da ke Sanagal da jami’an faransa suka yi a a1944 a sansanin sojin Thiaroye da ke wajen Dakar babban birnin Sanagal.

Bayan an saki shirin fim din, an tantance shi a Faransa.

Fim din san a karshe Moolaade, da aka saki a 2004 ya lashe gasar masu tantance fina-finan kasashen waje da suka fi kyau ta “Un certain regard” a Cennes, da kuma kambin Marrakech International.

Ayyukan daraktan dan kasar Sanagal na bayyana Afirka sama da yadda ake tunani. Hoto: OTHERS

Ousmane Sembene ya tafi ya bar ayyuka d asuka hada da gomman kagaggun labarai da zube tare da fina-finai 15.

Fim din Amil Shivji na karshe, Vuta Nk’vute, kai tsaye yana kama da ayyukan Sembene, inda yake nuna juyin juya hali da boren a gabar gabashin Zanzibar.

“FIna-finansa sun yi tasiri a kaina har zuwa yau, sun ba ni karfin gwiwa kuma suna zaburar da duk wasu masu shirya fina-finai iri na, na wannan zamanin.

"Muna samun damar bayyana labarai ba kawai saboda suna son fadar sub a, sai don bukatar su isa ga wadanda ya kamata,” in ji Amil Shivji.

TRT Afrika