Tonye Solomon: Dan Nijeriya ya kafa tarihi na wanda ya fi dadewa da kwallo a tsakar kansa

Tonye Solomon: Dan Nijeriya ya kafa tarihi na wanda ya fi dadewa da kwallo a tsakar kansa

GWR ya sanar da cewa Tonye ya hau matattakala 150 ya hau turakun gidan rediyo dauke da kwallo a tsakar kansa ba tare da ta fado ba.
Tonye ya shaida wa GWR cewa ya kafa wannan tarihi ne don karfafa wa sauran mutane gwiwar yin manyan abubuwa. Hoto GWR

A lokacin da Tonye Solomon dan Jihar Bayelsa a kudancin Nijeriya ya ce wa abokansa ya yi tafiyar kilomita 60 da kwallo a tsakar kansa ba ta fadi ba, babu wanda ya yarda da zancensa.

Da ya harzuka da ganin yadda mutane suka ki yarda da wannan bajinta, sai Tonye ya shirya tabbatar da hakan ta hanyar shiga kundin tarihi na duniya na Guinness World Record, a matsayin wanda ya yi bajintar hawa tsani da kwallo a tsakar kansa da ba wanda ya taba yi.

A ranar Laraba ne kundin GWR ya sanar da cewa Solomon ya kammala wannan kokari inda ya hau turakun gidan rediyo mai tsawon mita 76 da matattakala 150 da kwallon a tsakar kansa ba tare da ta fado ba.

Tonye ya shaida wa GWR cewa ya kafa wannan tarihi ne don kalubalantar kansa da kuma karfafa wa sauran mutane gwiwar yin manyan abubuwa.

Tonye ya hau kan turakun dauke da kwallo a kansa cikin minti 12 da rabi. Hoto: GWR

Ya shafe wata biyu yana atisayen hakan, inda yake ware lokaci sosai yana gwaji har sai lokacin da ya gamsu cewa ba zai fadi ba.

A wani bidiyo da GWR ya wallafa, an ga lokacin da Tonye ke hawa kan turakun a nutse, inda ya kammala hawa a cikin minti 12 da rabi kacal.

Bayan da ya kammala hawa matattakala 150 din, sai Tonye ya jeho kwallon kasa ya dunkule hannunsa yana murnar nasararsa.

"Ba abu ne mai sauki ba," ya ce. "Ina gode wa hukumar tsaro ta Civil Defence ta Nijeriya reshen Jihar Bayelsa, da suka ba ni dama na yi amfani da kayansu don yin wannan aiki."

Tonye yana Cibiyar Chukwuebuka Freestyle ta Chukwuebuka Ezugha, wadda ta samar da ayyuka da dama na bajinta don shiga tarihi da suka hada da Kid Eche da Vincent Okezie da Victor Richard Kipo da kuma Confidence Kipo.

"Na yi mamaki matuka saboda babu wanda ya taba yin irin hakan a baya," in ji Fish Jombo, wani mai gabatar da shiri a rediyo wanda ya shaidi yadda abin ya kasance, a cewar Guinness World Record.

Solomon ya shiga jerin 'yan Nijeriya da Afirka da suka yi wani abu na bajinta har sunayensu suka shiga kundin tarihi na Guiness Book of World Records.

TRT Afrika