Ngaira Mandara ya yi zane-zane kan birnin Dar es Salaam. Hoto: Ngaira  

Daga

Gaure Mdee

Dar es Salaam, wani birni mai cike da hada-hada a kasar Tanzaniya, an san shi ne ba kawai da kyakkyawan gabar teku ba da kasuwanni masu hada-hadar jama'a, amma kuma titunan birnin suna jan hankalin jama'a.

Tafiya a kewayen birnin tana da dadi, inda kyawawan wurare da kade-kade da kamshi suka hade da samar da wani abu na musamman.

Wannan ne ya ja hankalin mai zane-zane Ngaira Mandara ya yi zane-zane bisa dogaro da fahintarsa kan birinin da ya taso.

Ayyukan zane-zanensa da baje-kolin tufafi suna nuna yadda rayuwa take a birnin Dar es Salaam, birni mai mazauna fiye da miliyan biyar, kamar yadda hukumar Kididdiga ta Tanzaniya ta bayyana.

Soyayyar birnin

“Lokacin da na yanke shawarar zama cikakken mai sana'ar zane-zane, babban burina shi ne na yi zayyane-zayyane kan wani maudu'i," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Na samu kwarin gwiwar zana abubuwan da na sansu ko suka faru da ni. Daga mutanen da na hadu da su, zuwa wuraren da na taba ziyara da kuma abubuwan ban dariya da suka faru da ni."

Daya daga cikin abubuwan shi ne wani mutum mai tuka babur wanda ya dauko fasinja fiye da kima, inda ya goyo mutum uku a baya. Doka ta yarda ne ya dauki fasinja daya tal kawai.

Doka ta yarda masu babura su goya mutum daya tal ne a birnin Dar es Salaam.Hoto: Ngaira

"Ina tafiya a kan hanyar zuwa garin Makumbusho wata ina kan aiki kuma sai na ga wani dan Boda boda (wato dan acaba) ya goya mutum hudu. Kawai sai na ji sha'awar zana abin da na gani."

Ana kiran acaba da sunan Boda boda a kasashen yankin Gabashin Afirka kuma suna sana'ar na da farin jini — saboda yadda yake samarwa mutane sauki da biyan bukata.

“Wata rana kuma na ga wasu mutane suna shiga daladala (wato karamar bas) wanda wannan ma ya ba ni sha'awa. Daga nan ne, sai na mayar da hankali a birnin har ya zama abin da ake kira The Streets of Dar es Salaam (wato Titunan birnin Dar esSalaam).”

Birnin Dar es Salaam yana da kusan mutum miliyan biyar da ke rayuka a cikinsa. Hoto: Ngaira

Kowane birnin yana da al'adar da ta bambanta shi da saura kuma masu zane-zane suna zana abubuwan da ya sa birnin ya bambanta da saura a aikace-aikacensu.

"Na zabi birnin Dar es Salaam saboda a nan ne aka haife ni kuma na taso. Yayin da na ci gaba da zane-zane sosai, birnin da na taso ya kasance abin da yake ba ni kwarin gwiwa kan sana'ar zane-zaneta," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Mandara yana zana duk abin da ya dauki hankalinsa. Hoto: Ngaira 

Yin zane-zane da ke nuna yadda birnin da ka taso yake yana sa mutum yana tuna da asalinsa da kuma al'ummar da ya fito. Hakan kuma yana baki su ji birnin da mutanensa sun shiga ransa.

Kamar yadda Mandara ya ce: "Abubuwan da nake zanawa abubuwa ne da na gani a kowace ko kuma suka faru da ni. Daga mutanen da na hadu da su zuwa wuraren da na taba kai ziyara."

Birnin Dar es Salaam birni ne da ke da hada-hadar jama'a wanda yake gabar teku. Hoto: Ngaira.

Mandara yana aiki tare da wani dan Tanzaniya mai zane-zanen kwalliya Ally Remtullah wajen zayyana salon tufafi. Duk wani mutum daga birnin Dar es Salaam zai ji salon adon tufafin shi ma nasa ne.

"Na aiki kan zayyane-zayyane da dama da ya burge masu kai ziyara Zanzibar, kuma yayin da nake ci gaba da tafiye-tafiye, zan ci gaba da yin zane-zanen abin da na gani."

Mandara ya yi amannar cewa aikinsa zai sa mutane su fahimci yadda rayuwa take a Dar es Salaam. Hoto: Ngaira

A karshe, Mandara ya ce aikace-aikacensa na The Streets of Dar es Salaam ya kunshi abubuwan da suka faru a birnin wadanda 'yan baya za su so gani.

TRT Afrika