Man City ta yi murnar lashe Kofin Gasar Firimiya bayan ta doke Chelsea da ci 1-0

Man City ta yi murnar lashe Kofin Gasar Firimiya bayan ta doke Chelsea da ci 1-0

Julian Alvarez ne ya zura kwallon a fafatawar da suka yi a filin wasa na Etihad.
Kwallon ita ce ta 100 da City ta ci a Etihad a kakar wasa ta bana. Hoto/Reuters 

'Yan wasan Manchester City sun yi murnar lashe Gasar Firimiya karo na uku a jere ranar Lahadi, bayan sun doke Chelsea da ci 1-0.

Julian Alvarez ne ya zura kwallon a fafatawar da suka yi a filin wasa na Etihad.

Kwallon ita ce ta 100 da City ta ci a Etihad a kakar wasa ta bana, inda ta maimaita tarihin da ta kafa a 2018-19 - na zama kungiyar kwallon Ingila da ta ci kwallo mafi yawa a gidanta a dukkan gasa a kakar wasa daya.

Tun jiya City ta lashe Kofin bayan Arsenal ta sha kashi a hannun Nottingham Forest a wasan da suka yi.

Arsenal ta kwashe galibin kakar wasa ta bana tana bayan City da maki hudu inda take da sauran wasa daya bayan Forest ta doke ta da ci 1-0.

Yaran Pep Guardiola sun lashe Kofin sau biyar a cikin kakar wasa shida da suka gabata.

Baya ga wannan, City na da damar daukar karin Kofuna biyu a kakar bana: Kofin FA da kuma na Gasar Zakarun Turai a watan gobe.

Manchester United kadai ta taba yin irin wannan bajintar a kakar wasa ta 1998-99, kuma za ta fafata da ita a Wembley ranar 3 ga watan Yuni don neman daukar kofin FA.

Kazalika za ta gwabza da Inter Milan mako daya bayan haka a Istanbul domin neman lashe gasar Zakarun Turai karon farko.

TRT Afrika