Baykar, kamfani mai zaman kansa, ya dogara ga fitar da kayayyakin tsaro da ke ba shi kashi 83 na kudadne shiga tun 2003, ya kuma zama jagora a fannin tsaro da sufurin jiragen sama, kua jagora wajen fitar da kayayyakin / Hoto: AA Archive

Jirgin sama maras matuƙi na Bayraltar TB3 da kamfanin kayayyakin tsaro na Turkiyya Baykar ya samar ya kafa tarihin lulawa sama, ɗauke da injin da aka samar a cikin gida inda ya yi nisan mita 33,000 a sama a wajen wani gwaji da aka gudanar.

Sanarwar da kamfanin na Bayrak ya fitar a ranar Alhamis ta ce an ci gaba da gwada Bayraktar TB3 cikin nasara.

Bayan tashinsa na farko a ranar 27 ga Oktoban 2023 a yayin bukukuwan cika Turkiyya shekaru 100 da zama Jumhuriya, jirgin ya yi matsakaicin nisa da tashi sama sosai, a yanzu kuma Bayraktar TB3 UAV ya kammala Lulawa Sama Sosai a ranar Alhamis, tashi saman da ya kafa tarihi.

UAV ya samu nasarar kammala gwajin tashin a Cibiyar Tashi da Gwajin Tashin Jiragen Sama ta Akinci da ke gundumar Corlu a lardin Tekirdag tare da inji mai lamba PD-170 ƙirar kamfanin TUSAS na ko TEI na Turkiyya.

Kafa tarihin lulawa saman ya kusa na Bayraktar AKINCI TIHA, jirgin yaƙi maras matuƙi (UAAV) da Baykar ya samar wanda ya taɓa yin nisan ƙafa 45,118.

Jagoran fitar da kayayyakin sufurin jiragen sama

A ranar 26 ga Maris na wannan shekarar, kamfanin ya samu wata babbar nasara ta tashin ASELFLIR-500, wanda a duk duniya aka sani da aiki sosai da babu irin sa.

Jirgin mai fuka-fukai biyu da ake iya naɗe su, Bayraktar TB3 zai zama jirgin yaƙi maras matuki na farko da ke iya tashi daga gajeren titin jiragen sama kamar na jirgin TCG Anadolu.

Wannan ci gaba, tare da fasahar gani da sadarwa da yake da ita, ya sanya jirgin ya zama mai sauya fasalin amfani da jirage marasa matuƙa na yaƙi, yana da ƙarfin leƙen asiri da kai hari, wanda ke ƙara haɓaka ƙarfin nuna ƙwanjin Turkiyya.

Majalisar Fitar da Kayayyaki ta Turkiyya ta ce Baykar, kamfani mai zaman kansa, ya dogara ga fitar da kayayyakin tsaro da ke ba shi kashi 83 na kuɗaɗen shiga tun 2003, ya kuma zama jagora a fannin tsaro da sufurin jiragen sama, kuma jagora wajen fitar da kayayyakin.

Hukumar Kula da Masana'antun tsaro ta Turkiyya ta ce a 2023 kaɗai an fitar da kayayyakin da Baykar ya ƙera na dala biliyan 1.8, wanda shi ne sama da kashi 90 na kuɗaɗen da kamfanin ya samu a 2023.

A matsayin sa na kamfani mafi yawan fitar da UAV a duniya, Baykar na biyan buƙatar kaso 97.5 na dukkan kwangilar fitar da kaya waje, inda ya sanya hannu kan yarjeniyoyi a ƙasashen waje 34 inda 33 daga ciki suka sayi Bayraktar TB2 UAV, wasu ƙasashen tara kuma suka sayi Bayraktar AKINCI TIHA.

TRT World