'Yan sanda sun kama manyan 'yan jaridar Jaridar  Daily Sabah /Hoto: AA

'Yan sandan Jamus sun kai hari ofishin wata Jaridar Daily Sabah da ake wallafawa da harshen Turkanci inda suka kama manyan ma'aikatan wajen Ismail Erel da Cemil Albay, kamar yadda sauran ma'aikatan jaridar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Daraktan Sadarwa da Watsa Labarai na Turkiyya Fahrettin Altun, ya yi Allah-wadai da lamarin a ranar Laraba, yana mai cewa an kama ma'aikatan ne saboda wani korafi da wani mamba na Kungiyar Ta'addanci ta Fetullah (FETO) Cevheri Guven, ya shigar.

"Samamen, wanda aka kai da sanyin safiya kan gidaje da ofisoshin 'yan jaridar Turkiyya, tare da tsare su da kwace musu kayayyakin aiki saboda yin labaran da ke adawa da kungiyar FETO a Jamus, alama ce karara ta take 'yancin dan adam da kuma 'yancin watsa labarai," Altun ya wallafa a Twitter.

"Ba za mu yarda da wannan mataki na Jamus ba wanda wani yunkuri ne na rufe bakin 'yan jarida, kuma mun damu matuka kan yadda ake matsa wa 'yancin watsa labarai a kasar," ya ce.

Kamen ya jawo zanga-zanga daga kungiyoyin 'yan jarida na kasar, yayin da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta tuntubi hukumomin Jamus din tare da neman a yi gaggawar sakin 'yan jaridar, a cewar Anadolu.

"Muna kira ga hukumomin Jamus, da ke bai wa mambobin FETO kariya tare da yi wa ayyukan kungiyar ta'addancin uzuri, da su janye daga wannan babban laifin," Altun ya ce.

Ya nemi Jamus ta bai wa Turkiyya hadin kai tsakani da Allah a yakin da take yi da ta'addanci, sannan ta saki 'yan jaridar Turkiyyan da gaggawa.

Erel shi ne wakilin Jaridar Sabah a Turkiyya, shi kuma Albay shi ne shugaban Jaridar Sabah a Turai. Dukkansu suna aiki ne a birnin Frankfurt.

TRT World