Isra'ila ta yi luguden wuta a Rafah inda ta kashe Falasɗinawa 35 / Photo: AA

1446 GMT — Babban asibitin haihuwa na Rafah ya daina karɓar marasa lafiya: MDD

Babban asibitin kula da mata masu juna biyu a birnin Rafah da ke kudancin Gaza mai cunkoson jama'a ya daina karbar marasa lafiya, kamar yadda asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hukumar ta UNFPA ta ce asibitin haihuwa na Emirati, ya kasance yana karɓar haihuwar yara kimanin 85 a kowace rana daga cikin jimillar 180 da ake haifa a Gaza a kowace rana kafin barkewar fada tsakanin mayakan Falasdinawa da sojojin Isra'ila a wajen Rafah.

1434 GMT — Ma'aikatan EU sun yi zanga-zanga kan adawa da yaƙin Isra'ila a Gaza

Sama da ma'aikatan cibiyoyin Tarayyar Turai 100 ne suka hallara a Brussels a wata zanga-zangar adawa da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Masu zanga-zangar sun ajiye fararen ƙyallaye uku masu nuna alamar likkafani da jini a jikinsu a dandalin da ke wajen babban ofishin hukumar Tarayyar Turai da ke babban birnin Belgium.

A jikin ƙyallayen an rubuta kalmomin dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar EU da yarjejeniyar kisan kare dangi, a wani mataki na nuna rashin amincewa da yadda Isra'ila ta mayar da martani ga hare-haren da kungiyoyin gwagwarmaya karkashin jagorancin Hamas suka kai a ranar 7 ga Oktoba.

Wani ma'aikacin Hukumar Tarayyar Turai Manus Carlisle ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Muna wani taro na lumana, domin tsayawa tsayin daka wajen kare hakki da ka'idoji da ƙimar da cibiyoyin Turai suka ginu akai."

1243 GMT — An sake gano kabarin bai-ɗaya da gawarwaki 49 a Asibitin Al-Shifa na Gaza

Tawagar likitocin Falasdinu sun gano wani kabarin bai-ɗaya na uku a asibitin al-Shifa da ke Gaza, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin kasar ya sanar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya zuwa yanzu an tono gawarwakin mutane 49 daga cikin kabari, kuma ana ci gaba da kokarin neman karin wasu.

Ofishin yada labaran ya ce an gano kaburbura guda uku a asibitin al-Shifa, uku a asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, da kuma daya a cikin asibitin Kamel Adwan da ke arewacin Gaza.

“Akalla gawarwakin mutane 520 ne aka tono daga cikin kaburburan bai-ɗaya bakwai,” in ji sanarwar.

0937 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a Rafah inda ta kashe Falasɗinawa 35

Aƙalla Falasɗinawa 35 Isra’ila ta kashe da raunata wasu 129 a yayin wani mummunan hari da ta kai Rafah a sa’o’i 24 da suka wuce.

Sojojin sun kashe mutanen ne ta hanyar amfani da jirgin sama domin yi musu luguden wuta.

Majiyoyi na ɓangaren kiwon lafiya sun ce Falasɗinawa da aka kashe ƴan gudun hijira ne waɗanda ba su jima da zuwa asibitin Kuwait ba da ke Rafah, inda majiyar ta ce akwai yara da mata a cikinsu.

0018 GMT — Isra'ila ta kashe mutum bakwai 'yan gida ɗaya a wani hari da ta kai gidansu a Gaza

Asibitin Al-Ahli ya bayar da rahoton cewa, Isra'ila ta kashe akalla mutane bakwai 'yan gida daya tare da raunata wasu da dama a wani harin da ta kai ta sama a wani gida a birnin Gaza.

Asibitin Al-Ahli ya sanar da cewa, an samu asarar rayuka a harin da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke arewacin birnin da ya lalace, kuma shaidu sun kuma bayar da rahoton cewa, an kai hare-hare a wasu wurare a yankin da aka yi wa ƙawanya, musamman a kusa da Rafah.

0014 GMT — Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawan sun yi artabu da sojojin Isra'ila a Rafah

Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojojin Isra'ila da 'yan gwagwarmayar Falasdinawa a gabashin birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Kazalika jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari kan hedikwatar karamar hukumar da ke kusa da kan iyaka da Masar da kuma gidaje, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ruwaito.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas reshen kungiyar Al-Qassam Brigades a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, sun kai hari kan tankar Merkava ta Isra'ila inda suka cinna mata wuta.

Dakarun sun ƙara da cewa sun yi arangama da sojojin Isra'ila da ke cikin wani gini a unguwar Shouka a Rafah.

A wata sanarwa da suka fitar, sun ce sun kai wa sojojin Isra'ila hari da makami mai linzami mai cin gajeren zango na Rajoum da kuma harsasai masu girman gaske.

TRT Afrika da abokan hulda