Tsawon lokaci, Faransa ta kasance ƙasar da ake zuwa gudun hijira, har daga kasashen da ta yi wa mulkin mallaka na Arewaci da Yammacin Afirka. / Hoto: AFP

'Yan ƙasar Faransa Musulmai ƙwararru da suke 'yan asalin wasu yankunan, mafi yawan su 'ya'yan 'yan gudun hijira, na barin Faransa don neman ayyuka masu tsoka a waje, musmaman a birane irin su Landan ko New York ko Montreal ko Dubai, kamar yadda wani sabon bincike ya bayyana.

Marubutan "France, you love it but you leave it' (Faransasa, kana son ta kana barin ta), da aka buga a watan da ya gabata, sun ce yana da wahala a iya ƙiyasta cikakken adadinsu.

Amma sun gano cewa kashi 71 ko sama da haka na mutane 1,000 da suka bayar da amsar tambaoyin da aka yi musu ta yanar gizo sun ce sun bar Faransa ne saboda nuna wariya da nuna bambanci.

Adam, wanda ya ce kar a yi amfani da sunansa na biyu, ya fada wa AFP cewa sabon aikin da ya samu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya buɗe masa sabon shafi na rayuwa.

Ya ce a Faransa "kana bukatar yin aiki ninki biyu idan aka ce ka fito daga al'umma marar rinjaye".

Ya kuma ce yana godiya da ilimin da ya samu a Faransa kuma yana kewar abokai da iyali da al'adun ƙasar masu yawa, inda a nan ne ya girma.

Amma ya ƙara da cewa yana farin ciki da ya bar ƙasar, saboda "Nuna ƙyama ga Musulunci" da "tsararren nuna wariya" inda za ka ga 'yan sanda na tare ka ba tare da dalili ba.

Tsawon lokaci Faransa ta kasance kasar da ake zuwa gudun hijira, har daga kasashen da ta yi wa mulkin mallaka na Arewaci da Yammacin Afirka

Amma a yau 'ya'yan Musulmai d asuka yi gudun hijira zuwa Faransa don inanta rayuwarsu na fadin suna rayuwa a tsakanin al'ummar da ke gaba da su.

Sun ce tsarin ƙasar, da ba ruwanta da addini, wadda ta haramta amfani da alamomin dukkan addinai a makarantu ciki har da saka hijabi da dogayen riguna, ya zama kamar tsari ne da ya ta'allaka kan cusgunawa matan Musulmai kawai.

Wani Musulmi ɗan ƙasar Faransa ɗan shekara 33 da a fito daga Morocco, ya faɗa wa AFP cewa, shi da matarsa mai juna biyu na shirin yin gudun hijira zuwa "ƙasa mai zaman lafiya sosai" a kudu maso-gabashin Asiya.

Ya bayyana buƙatar barin ƙasar da "wannan babban ɓacin rai", inda kuma labaran talabijin suke harar Musulmai a matsayin masu laifin da ba su suka yi aikata ba.

Ma'aikacin na kamfanin fasaha da ya koma Paris da zama bayan ya girma a ɗaya daga ƙananan yankunan wajen birnin, ya ce tsawon shekara biyu kenan yana zaune a gida guda.

Ya ce "Amma har yanzu suna tambaya ta me ka ke yi a cikin gidana."

"Wannan wulakanci ne."

Ya ƙara da cewa "irin wannan wulaƙancin da ake yi mana koyaushe ya fi komai ciwo ganin yadda nake bayar da gudunmuwa ga al'umma, sannan na ke biyan haraji da yawa saboda yawan albashina."

'Yan ƙasa marasa muhimmanci

A 1978 dokokin Faransa suka haramta tattara bayanan launin fata ko asalin mutum ko yarensa ko addini, wanda da wahala a iya samun alƙaluman nuna wariya.

Amma matashi "da aka gano Balarabe ko bakar fata ne" zai iya fuskantar binciken waye shi ninki ashirin sama da sauran jama'a, wani 'yancin bincike na Faransa da aka assasa a 2017.

Masu sanya idanu kan nuna wariya na cewa nuna wariyar launin fata na raguwa a Faransa, inda kashi 60 na jama'ar faransa ke bayyana cewa ba dukkan su ne suke nuna wariya ba.

Amma har yanzu ana ci gaba da hakan, idan za a ɗauki aiki idan ka ƙara sunan Faransa a sunanka ka fi samun dama da kashi 50 sama da wanda ba shi da irin sunan kasar ko wanda ya fito daga arewacin Afirka.

Wani ɗan Faransa ɗan asalin Aljeriya mai shekara 30 da ya yi karatun digiri na ɗaya da na biyu a manyan makarantu, ya fada wa AFP cewa zai bar ƙasar a watan Yuni don yin aiki a Dubai saboda Faransa ta zama rikitacciyar ƙasa.

Ma'aikacin banki kan harkokin zuba jari, ɗan gidan wani mai aikin tsafta ɗan Aljeriya da ya girma a Paris ya faɗi cewa yana jin daɗin aikinsa, amma ya fara tunanin shi ma zai ƙara gaba.

Ya kuma ce siyasar Faransa na ƙara tsauri a 'yan shekarun nan.

"Lamarin a Faransa ya munana sosai," in ji shi, yana sukar wasu mutane da ke yi wa kowa kuɗin goro a ɓangaren bayar da gidaje haya.

"Tabbas Musulmai 'yan ƙasa ne marasa ƙima da daraja a Faransa".

Adam, ƙwararre da ke bayar da sahwarwari, ya ce Musulmai a Faransa da suke da kuɗi sosai kuma suke yin hijira wani ɓangare ne na matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce "Idan muka kalli Faransa a yau, sai mu ji mun talauce."

TRT World