Wani sojan Isra'ila yana wucewa a kusa da tankokin yaƙin da aka jibge a kan iyakar Isra'ila da Gaza.  / Hoto: Reuters

1504 GMT — Shugaban sojojin Isra'ila ya amince da shirin kai hari a Rafah

Shugaban rundunar sojojin ƙasa ta Isra'ila Herzi Halevi ya amince da shirye-shiryen ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a Rafah da ke kudancin Gaza, a cewar kafofin watsa labaran Isra'ila.

Ya bayyana amincewar tasa ne duk da ƙoƙarin da masu shiga tsakani suke yi na ganin an ƙulla yarjejeniyar tsagaita tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa.

An amince da shirye-shiryen ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a Rafah ne yayin ganawar da aka yi tsakanin Halevi, da kwamadan soji na kudacin Isra'ila Yaron Finkelman da sauran manyan kwamandojin rundunonin tsaron Isra'ila, a cewar jaridar The Jerusalem Post.

Hakan na faruwa ne bayan Ministan Tsaron Isra'ila mai tsattsauran Bezalel Smotrich ya yi barazanar rusa gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu idan ya amince da tayin Masar na tsagaita wuta a Gaza.

0945 GMT — Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna fiye da 500 sun mamaye Masallacin Ƙudus ranar hutun bikin Passover

Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna fiye da 500 ne suka mamaye Masallacin Ƙudus a yayin da ake hutun bikin Passover.

"Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna fiye da 500 sun yi kutse a Masallacin Ƙudus ta Ƙofar Mugharbah inda suka riƙa yin izgilanci sannan suka yi ta rawa salon Talmud a harabar masallacin," a cewar hukumar Musulunci ta Islamic Endowments Authority a wata sanarwa da ta fitar.

Ta ƙara da cewa 'yan kama-wuri-zaunan sun yi kutsen ne bayan sun samu kariya daga 'yan sandan Isra'ila, waɗanda suka ɗauki tsauraran matakan tsaro a Tsohon Birni da Masallacin Ƙudus.

'Yan kama-wuri-zaunan sun yi kutsen ne bayan sun samu kariya daga 'yan sandan Isra'ila, waɗanda suka ɗauki tsauraran matakan tsaro a Tsohon Birni da Masallacin Ƙudus. / Photo: AA

0500 GMT — Taron Saudiyya zai mayar da hankali kan hare-haren da Isra'ila take kai wa al'ummar Gaza

Ƙasar Saudiyya za ta karɓi baƙuncin taron tattalin arziki na World Economic Forum a yau Lahadi ko da yake zai mayar da hankali kan hare-haren da Isra'ila take kai wa Gaza da kuma jijiyoyin wuyar da ake tayarwa a Gabas ta Tsakiya.

Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken, da shugabannin Falasɗinawa da shugabannin wasu ƙasashe za su yi ƙoƙarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar tsagaita tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas a taron da za a gudanar a Riyadh, babban birnin ƙasar.

"Duniya tana cikin tsaka-mai-wuya a yau, inda take ƙoƙarin ganin an samar a tsaro da ci gaba mai ɗorewa," a cewar ministan tsare-tsare na Saudiyya Faisal al-Ibrahim a wajen taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar game da taron na yau.

"Za mu gana ne a lokacin da kuskure ɗaya tilo daga gare mu yana iya ta'azzara ƙalubalen da muke ciki."

Ana fargabar cewa kimanin mutum 8,400 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine waɗanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta. / Hoto: Reuters

0006 GMT —Hezbollah ta harba makamai masu linzami a matsugunan Isra'ila da ke kan iyakar Lebanon

0006 GMT — Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba gomman makamai masu linzami a matsugunan Isra'ila da ke kan iyakar Lebanon.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta harba gomman makamai masu linzami samfurin Katyusha a matsugunan Meron da ke kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

Ta ce ta ɗauki matakin ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila take kai wa ƙauyukan da ke kudancin Lebanon, musamman ƙauykan Qaouzah, Markabta da Srobbine.

Gidan rediyon rundunar sojin Isra'ila ya wallafa saƙo a shafin X da ke cewa dakarunsu sun sa ido kan rokoki 25 da aka harba zuwa yankin Meron na Lebanon, kuma an kakkaɓo wasu yayin da wasu suka faɗa a yankunan da babu jama'a.

Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya a yayin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hari a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza ranar 27 ga watan Afrilu, 2024. / Hoto: AFP

2330 GMT — Kamfanin X ya dakatar da shafin jikan Mandela saboda goyon bayan Gaza Flotilla

Kamfanin soshiyal midiya na X ya dakatar da shafin jikan Nelson Mandela bayan ya yi hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu inda ya nuna goyon baya shirin International Freedom Flotilla da ke neman kai kayan agaji ga Falasɗinawan Gaza.

Nkosi Zwelivelile Mandela ya bayyana goyon bayansa ga International Freedom Flotilla da ke shirin kai agaji Gaza tare da kawar da ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin.

A farkon wannan makon ne ya isa Istanbul domin hakartar taro karo na 5 mai taken Inter-Parliamentary Jerusalem Platform and support the preparations of the International Freedom Flotilla a Turancin Ingilishi.

Nkosi Zwelivelile Mandela ya bayyana goyon bayansa ga International Freedom Flotilla da ke shirin kai agaji Gaza tare da kawar da ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin./ Hoto: AA
TRT Afrika da abokan hulda