Kusan mutum huɗu cikin biyar ‘yan Birtaniya na kallon Isra’ila a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar duniya, kamar yadda wani babban bincike da Cibiyar Nazarin Al’umma ta Ƙasa (National Centre for Social Research – NatCen) ta wallafa a cikin rahotonta na British Social Attitudes.
Sakamakon binciken ya nuna cewa kashi 78 cikin 100 na waɗanda aka gudanar da binciken a kansu na ganin Isra’ila a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar duniya.
Wannan adadi ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da kashi 48 cikin 100 da aka samu a shekarar 2005.
Rahoton ya ce wannan kaso ya haura na ƙasashen Iran da Amurka, inda kashi 75 cikin 100 na ’yan Birtaniya ke kallon Iran a matsayin babbar barazana, yayin da kashi 74 cikin 100 ke da irin wannan ra’ayi kan Amurka.
Kazalika rahoton wanda aka yi take da ‘‘Duniyar da ke ƙara zama mai haɗari: Ra’ayoyin Birtaniya kan tsaro, kariya da ƙawancen ƙasashen duniya’’ ya yi nazari kan yadda ra’ayoyin al’ummar ƙasar suka sauya dangane da barazanar tsaro a duniya.
Rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya
Haka kuma “ƙimar Isra’ila ta zube sakamakon rawar da ta taka a rikice-rikicen baya bayan nan a Gabas ta Tsakiya,” a cewar rahoton, yana mai bayyana yadda al’ummar Birtaniya suka nuna damuwa kan ƙasar sosai a cikin ’yan shekarun nan.

Binciken ya nuna cewa adadin ’yan Birtaniya da ke kallon Isra’ila a matsayin babbar barazana ya kai kashi 73 cikin 100 a tsakiyar shekarar 2024, bayan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya haddasa mummunar barna a yankin.
Sai dai wannan adadi ya ragu zuwa kusan kashi biyu bisa uku a shekarar 2025, kafin ya sake tashi zuwa kashi 78 cikin 100 a wani binciken da aka gudanar a lokacin bazara ta shekarar 2026, bayan hare-haren sama na haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.
Binciken ya kuma nuna bambancin ra’ayoyi tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa, duk da cewa mafi yawan magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar ƙasar sun nuna matuƙar damuwa kan Isra’ila.
Magoya bayan Jam’iyyar Green ne suka fi kallon Isra’ila a matsayin babbar barazana, inda kashi 88 cikin 100 suka bayyana hakan, yayin da magoya bayan Jam’iyyar Labour suke da kashi 84 cikin 100.
A ɓangaren magoya bayan Jam’iyyar Liberal Democrats, kashi 79 cikin 100 ne suka bayyana irin wannan ra’ayi, yayin da kashi 70 cikin 100 na magoya bayan Jam’iyyar Conservative suke da kashi 62 cikin 100 na magoya bayan, yayin da kuma Reform UK suka ce Isra’ila babbar barazana ce ga zaman lafiyar duniya.


















