| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Ministan harkokin wajen Iran ya kawar da yiwuwar tattaunawa da Amurka
Araghchi ya bayyana cewa babu wata sabuwar tattaunawa bayan Amurka ta kai wa Iran hari duk da 'gagarumun ci-gaba' da aka samu a tarukan da aka yi a Geneva cikin watan Fabrairu.
Ministan harkokin wajen Iran ya kawar da yiwuwar tattaunawa da Amurka
Araghchi ya ce Tehran ta dena tunanin tattaunawa da Washington / Reuters / Reuters

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yanke ƙauna kan yiwuwar sake tattaunawa da Amurka bayan abin da ya bayyana a matsayin wani lamari "mai tsabar muni."

Da yake magana a wata hira da kafar watsa labarai ta PBS News ranar Litinin, Araghchi ya yi tsokaci kan ko sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, zai buɗe ƙofar sabuwar tattauna ko kuma tsagaita wuta.

Ya ce zai "yi sauri da yawa a yi wani tsokaci” kan lamarin.

"Amma ba na tunanin maganar sake tattaunawa da Amurkawa ko yarjejeniya da Amurkawa za ta kasance a cikin ajandarmu bayan Amurkawa sun aikata mummunan lamari," in ji Araghchi .

Ya yi ishara ga yaƙin kwanaki 12 da aka yi a watan Yunin da ya gabata a lokacin da Isra’ila da dakarun Amurka suka kai hari kan tashoshin nukiliyar Iran yayin da ake tattaunawa tsakanin Tehran da Washington .

Da yake magana game da zagaye na baya bayan nan na tattaunawa a Geneva a ƙarshen watan Fabrairu, Araghchi ya ce ɓangarorin biyu sun bayyana tattaunawar a matsayin mai alamar alfanu a tsarin shiga-tsakani na ƙasar Oman.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran ta yi iƙirarin kashe sojojin Amurka 500 a cikin kwanaki biyar na yaƙi

"Amma kuma, bayan zagaye uku na tattaunawa, kuma bayan tawagar Amurka a tattaunawar ta bayyana da kanta cewa mun samu gagarumin ci-gaba, duk da haka, sun yanke shawarar kai mana hari," in ji shi.

"Saboda haka ba na tunanin sake tattaunawa da Amurkawa zai kasance a cikin ajandarmu."

Tashe-tashen hankula na yanki

Da yake magana game da katse harkoki a kasuwancin man duniya, Araghchi ya ce ba Iran ba ce ta janyo koma-baya ga yadda ake samar da man fetur da kuma jigilarsa a duniya.

"Wannan ba laifinmu ba ne. Wannan ba tsarinmu ba ne," in ji shi.

Ya ce hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai ne suke janyo tsaikon.

Araghchi ya ce waɗannan hare-haren sun sa yankin na ƙara zama maras zaman lafiya kuma mara tsaro.

"Wannan shi ya sa tankoki da jiragen ruwan suke tsoron wucewa ta mashigin ruwan Hormuz," in ji shi.

Araghchi ya yi watsi da zarge-zargen cewa Iran tana katse jigilar mai da gangan ta hanyar kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke safarar makamashi a yankin.

"Muna fuskantar wani mataki na tsangwama, wanda kwata-kwata bai dace da doka ba, kuma abin da muke yi shi ne matakin kare kai, wanda ya dace da doka," in ji shi.

Ya ƙara da cewa Tehran ta gargaɗi ƙasashen yankin cewa idan Amurka ta kai hari kan Iran kai-tsaye, Iran za ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin Amurka da kayayyakinta a faɗin yankin.

"Kuma sakamakon hakan, yaƙin zai bazu zuwa dukkan yankin," in ji Araghchi.

"Ba mu muke da alhaƙin wannan ba."

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'