| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Trump ya yi barazanar ɗaukar 'mataki mai tsanani' kan Iran yayin da Netanyahu ya tafi Washington
Shugaba Trump ya nuna yiwuwar tura ƙarin dakaru da jirgin ruwa mai ɗauke da jiragen saman yaƙi na Amurka kusa da Iran yayin da Netanyahu ya isa domin tattaunawa ta musamman, kamar yadda kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito.
Trump ya yi barazanar ɗaukar 'mataki mai tsanani' kan Iran yayin da Netanyahu ya tafi Washington
Shugaban Amurka ya ce ko Iran ta shiga yarjejeniya ko kuma ‘zai zama dole mu mu yi wani abu mai tsanani sosai’ / AP / AP
17 awanni baya

Shugaban Amurka Trump yana tunani kan tura sojojin ruwa da jirgi mai ɗauke da jiragen yaƙi na biyu kusa da Iran yayin da yake shirin yiwuwar ɗaukar matakin soji, kamar yadda kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito.

Matakin yana zuwa ne yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke hanyarsa ta zuwa Washington domin ganawa da Trump yayin da aka sabunta tattaunawar Amurka da Iran.

Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta Axios a wata hira cewa yana “tunanin” tura dakarun ruwa da jirgin sama mai ɗaukar jiragen yaƙi zuwa Gabas Ta Tsakiya.

“Muna da ayarin jiragen yaƙi da ke kan hanyarsu ta zuwa yankin kuma ƙarin wani (ayarin) zai iya fara tafiya,” a cewarsa.

Masu AlakaTRT Afrika - Shugaban Iran Pezeshkian ya bayyana tattaunawar nukiliya da Amurka a matsayin 'ci gaba' ga Tehran

Jirgi mai ɗaukar jiragen yaƙin zai haɗu da jirgin yaƙi na ruwa na USS Abraham Lincoln da ayarinsa na dakaru da jiragen yaƙi na ruwa, wanda yake yankin.

Ayarin dakarun da jiragen yaƙin ya haɗa da jiragen yaƙi na sama da makamai masu linzami da jiragen ruwa, wani lamari mai kama da yadda aka tura kayan yaƙi a lokacin yaƙin kwana 12 na shekarar da ta gabata.

Tura kayayyakin sojin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sake buɗe ƙofar diflomasiyya tsakanin ɓangarorin biyu.

Jami’an Amurka da Iran sun gana ranar Juma’a Oman a karon farko tun rikicin watan Yunin da ya gabata.

Kafofin watsa labaran Amurka sun ambato Trump yana cewa, “Ko mu ƙulla yarjejeniya ko kuma zai kasance dole mu yi wani abu mai tsanani kamar na lokacin da ya gabata.”

Ya ce ana tsammanin a fara zagaye na biyu na tattaunawa a mako mai zuwa.

Shugaban Amurka ya bayyana fata na kaffa-kaffa.

“A lokacin da ya gabata ba su yi abin da ya dace ba . Sun tsaurara da yawa. A halin yanzu tattauwanar ta sha bamban,” in ji shi, yana maa iƙirarin cewa Iran “na matuƙar so ta ƙulla yarjejeniya ” kuma tana mayar da hankali sosai kan tattaunawa fiye da yadda ta yi a zagayen tattaunawa ta baya saboda barazanar soji.

Tehran ta jaddada cewa za ta tattauna game da shirin nukiliyarta ne kawai kuma ba za ta sarayar da ‘yancinta na sarrafa yuraniyom ba.

Rumbun Labarai
Khamenei ya yi gargaɗi kan yaƙin yanki idan Amurka ta kai hari kan Iran
Iran ta ayyana rundunonin sojin ƙasashen Turai a matsayin 'ƙungiyoyin ta'addanci'
A 'shirye' Iran take don 'yarjejeniyar nukiliya ta gaskiya da adalci': Ministan Harkokin Wajen Iran
Waɗanne abubuwa ne za su iya faruwa idan Amurka ta kai hari Iran?
Iran ta ce duk maƙociyar da ta bari aka yi amfani da ita wurin kai mata hari 'abokiyar gaba' ce
Isra'ila na karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, ta ci gaba da kai hari
Manyan jami'an China sun tattauna da Ƙungiyar OIC a yanayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara muni
Yaƙin da ake yi da ta'addancin Daesh yana ƙara ƙarfi: Erdogan
Iran ta gargaɗi Amurka: 'Za mu ɗauki kowane irin hari a matsayin cikakken yaƙi a kanmu'
Turkiyya ba ta goyon bayan tsoma bakin ƙasashe waje a kan Iran – Erdogan
Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya kai  4,000: Rahoto
Syria ta cim ma tsagaita wuta don karɓe iko da arewa maso gabas daga hannun ‘yan ta’addan YPG
Iran ta sha alwashin gwabza yaƙi da duk ƙasar da ta yi gangancin kai wa Khamenei hari
Syria ta ayyana harshen Kurdanci a matsayin 'harshen ƙasa', sannan ta ba Kurdawa haƙƙin 'yan ƙasa
An buɗe sararin samaniyar Iran bayan rufe shi na wucin-gadi
Trump ya yi barazanar ‘ɗaukar tsattsauran mataki’ idan Iran ta rataye masu zanga-zanga
'Taimako yana zuwa' in ji Trump ga masu zanga-zanga a Iran
Iran ta ce a 'shirye' take ta tattauna da Amurka amma kuma ta 'shirya wa yaƙi'
Kungiyar ta'addanci ta YPG ta ƙwace iko da wani asibiti a Aleppo, ta kori ma'aikatan lafiya
Ma'aikatar Tsaron Syria ta sanar da tsagaita wuta a wasu unguwannin Aleppo