Amurka ta kai hari kan mayaƙan Daesh a Nijeriya, in ji Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasarsa ta kai hare-haren a kan 'yan ta'adda na ƙungiyar ISIS (Daesh) da ke arewa maso yammacin Nijeriya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa ta ƙaddamar da hare-hare kan mayaƙan ƙungiyar ISIS a Arewa Maso Yammacin Nijeriya waɗanda ya ce sun kwashe shekaru da dama suna kashe Kiristoci.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Alhamis, Donald Trump ya ce "a daren nan, bayan umarnin da na bayar a matsayina na Babban Kwamanda, Amurka ta ƙaddamar da gagarumin hari kan 'yan ta'adda na ISIS (Daesh) a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, waɗanda suke kai hari tare da kashe, musamman Kiristoci da ba su ji ba ba su gani ba."
Ya ƙara da cewa, "A baya na yi gargaɗi cewa idan waɗannan ‘yan ta’adda ba su daina kashe Kiristoci ba, za su ɗanɗana kuɗarsu, kuma a daren nan, abin da ya faru ke nan."
Trump ya ce Ma’aikatar Yaƙi ta Pentagon ta ƙaddamar da hare-hare masu ƙarfi, “waɗanda Amurka ce kawai take da ƙarfin kai su."
Daga bisani, Cibiyar Bayar da Umarni ta Amurka da ke Afirka wato AFRICOM ta wallafa wani saƙo a shafin X, tana mai yin ƙarin haske cewa an kai harin ne a "Jihar Sokoto inda aka kashe 'yan ta'addan ISIS da dama".
"Munanan hare-haren da aka kai kan ISIS sun nuna ƙarfin sojinmu da kuma alwashinmu na kawar da duk wata barazanar ta’addanci a kan Amurka a gida da waje," in ji saƙon.
A makon nan ne wasu rahotanni suka nuna cewa Jiragen saman Amurka sun fara gudanar da zirga-zirga don yin nazari da tattara bayanan sirri a manyan sassan Nijeriya tun daga karshen watan Nuwamba.
A watan Nuwamba, Trump ranar ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasarsa ta soma shirye-shiryen yiwuwar kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Trump ya bayar da umarnin ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
A martaninta, gwamnatin Nijeriya ta musamman zarge-zargen, kuma Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa tun lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga kowane yanki da addini.