Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Jumma’a ya ce Kiristocin Nijeriya suna fuskantar "barazanar gushewa" sakamakon kisan gillar da ake yi musu lamarin da ya ce shi ya sanya shi saka ƙasar a cikin ƙasashen da "ake matuƙar nuna damuwa a kansu".
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Trump ya ɗauki matakin ne duk kuwa da cewa kwanakin baya mai ba shi shawara kan harkokin Afirka, Mossad Bullos, ya yi watsi da iƙirarin da ke cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.
"Kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu kaifin kishin Musulunci ne ke aikata wannan kisan gillar. Don haka na ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake matuƙar damuwa a kanta".
Kazalika Trump ya ce ya bai wa 'yan majalisar wakilan Amurka Riley Moore da Tom Cole umarnin ƙaddamar da bincike “nan-take game da batun kuma su kawo mini rahoton” sakamakon binciken.
Kawo yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta yi martani game da waɗannan kalamai ba. Amma a baya ta ƙaryata iƙirarin da ɗan majalisar dattawan Amurka Ted Cruz ya yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.









