Daraktan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci a Ghana (NCTFC) Birgediya Janar Timothy Dr Ba-Taa-Banah ya ce ƙasar Ghana za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana game da masu tsattsauran ra’ayi da ke tayar da zaune tsaye duk da cewa ba a samu wani hari ba a ƙasar.
Ya bayyana cewa nasarar da ƙasar ta samu ta rashin fuskantar hari ta samo asali ne daga duƙufa wajen ɗaukar matakan kandagarki da aka aiwatar tsawon shekaru, waɗanda kuma za a ɗore da su.
Birgediya Janar Ba-Taa-Banah ya bayyana haka ne a wajen taron kwanaki uku na masu ruwa da tsaki a birnin Accra, domin sake nazari kan tsarin yaƙi da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi.
“Rashin samun asarar rai a ƙasarmu ya faru ne sakamakon haɗakar matakai masu kyau da aka ɗauka. Amma hakan ba yana nufin ba za a iya kai mana hari ba ne, ko kuma ya ba mu damar yin sakaci. Dole ne dukkan masu ruwa da tsaki a wannan tafiya su kasance cikin shiri da sanya ido,” in ji shi.
Taron, wanda Gwamnatin Ghana ta shirya ta hannun NCTFC tare da tallafin Shirin Raya Ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), ya haɗa da wakilai daga hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin addini, da na matasa.
Mahalarta taron suna sake nazarin tsarin na shekarar 2019 ne domin tabbatar da dacewarsa da sabbin barazanar da ke tasowa, waɗanda suka haɗa da yaɗa labaran ƙarya ta hanyar fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI), dabarun samar da kuɗaɗen ta’addanci, da kuma karkata ra’ayin mutane zuwa tsaurara ra’ayi ta intanet.
Birgediya Janar Ba-Taa-Banah ya ce Afirka ta fuskanci hare-haren ta’addanci da dama tun daga karshen shekarun 1990, inda ya bayar da misali da abubuwan da suka faru a Tanzaniya da Kenya.
Ya yi gargaɗin cewa ko da yake Ghana ba ta fuskanci matsaloli sosai ba, ƙaruwar masu tsattsauran ra’ayi a ƙasashe maƙota, musamman a yankin Sahel, na buƙatar sanya ido na dindindin.
Ya ƙara da cewa, “Idan ba a samu tattalin arziki mai karfi ba, ba za a iya tinƙahon samun tsarin tsaro mai ƙarko ba... wataƙila ba mu yi asarar rayuka kai-tsaye daga Paga har zuwa Aflao ba, amma hakan ba yana nufin cewa tattalin arzikin ƙasar bai samu naƙasu ba.”
Taron sake nazarin ya shafi yankunan mulki 11 ne cikin 16, tare da tuntuɓar ’yan ƙasa, ƙungiyoyin ƙwararru, da masu ruwa da tsaki na gida.
Ana sa ran jami’an tsaro za su tantance yadda aka aiwatar da tsarin, su gano matsalolin da aka samu, sannan su fitar da shawarwari don ƙarfafa matakan riga-kafi da na mayar da martani daga ɓangaren Ghana.
Miss Shaima Hussein, Mataimakiyar Wakiliyar UNDP ta yaba wa matakin Ghana na tafiya da kowa da kowa, inda ta bayyana muhimmancin matasa, mata, da al’ummomi wajen yaƙi da masu tsattsauran ra’ayi.












