| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Shugaban Ghana ya faɗa a New York cewa Amurka tana goge tarihin baƙar-fata
Tun da ya koma kan mulki, Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da hankali kan cibiyoyi na al’adu da na tarihi - daga gidajen tarihi da wuraren shaƙatawa- domin cire abin da ya kira aƙidar "ƙin jinin Amurka."
Shugaban Ghana ya faɗa a New York cewa Amurka tana goge tarihin baƙar-fata
Shugaban Ghana John Dramani Mahama / Reuters
4 awanni baya

Shugaban Ghana John Dramani Mahama, da yake jawabi a birnin New York ranar Talata ya soki gwamnatin Amurka kan abin da ya kira mayar da goge tarihin baƙar-fata wani abun da ba shi da wata matsala, yana mai gargaɗin cewa irin waɗannan manufofin za su iya yin tasiri mai yawa a wasu wurare.

Tun da ya koma kan mulki, Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da hankali kan cibiyoyi na al’adu da na tarihi - daga gidajen tarihi da wuraren shaƙatawa- domin cire abin da ya kira aƙidar "ƙin jinin Amurka."

Bayanansa da umarnin da yake bayarwa sun sa an cire ababen tunawa da cinikin bayi da kuma dawowa da butum-butumi na masu goyon bayan cinikin bayi da sauran matakai da masu rajin kare hakkin bil’adama suka ce za su iya warware ci-gaban da aka shafe gomman shekaru ana samu a fannin zamantakewa.

"Waɗannan manufofin suna zama ababen kwaikwayo ga gwamnatoci da kuma cibiyoyi masu zaman kansu," in ji Mahama, yayin da yake magana a wani taron biyan diyya kan cinikin bayi da aka yi a Majalisar Ɗinkin Duniya. "Aƙalla, sannu a hankali suna mayar da goge tarihi a matsayin wani abu da ba shi da wata matsala."

Masu AlakaTRT Afrika - Ghana ta buƙaci taimakon MDD don warware batun cinikin bayi saboda ƙarfafa ƙoƙarin neman biyan diyya

Mahama ya ce a Amurka, ana cire darrusan tarihin baƙar-fata daga manhajar karatu, kuma ana bai wa makarantu umarnin daina koyar da "gaskiyar abin da ya faru lokacin cinikin bayi da raba baƙaƙe da farare da kuma wariyar launin fata", kuma ana haramta littatafai da ke magana a kan batun.

Fadar White House ba ta mayar da martani nan-take ba ga buƙatar da aka yi ta yi tsokaci kan batun.

Mahama, wanda a bara ya yi shelar wata yarjejeniya ta karɓar ‘yan asalin yammacin Afirka da aka taso ƙeyar su daga Amurka, ya taɓa sukar Trump kan iƙirarinsa na bogi cewa ana yi wa fararen-fata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu, yana mai kiransu cin mutunci ga duk ‘yan Afirka.

Mahama ya je New York domin gabatar da wani ƙudiri a zauren MƊD ranar Laraba domin ta amince da cinikin bayi daga Afirka zuwa Turai da Amurka a matsayin "laifi mafi muni a tarihin bil’adama" da kuma kira da a biya diyya.

Ƙasar ta yammacin Afirka tana gaba gaba wajen neman a biya diyya, wani mataki da yake ƙara ƙarfi a cikin ‘yan shekarun nan, duk da cewa an fara samun ƙin amincewa da hakan.

Wasu shuwagabannin ƙasashen yamma sun ƙi a tattauna maganar da su, inda masu suka ke cewa bai kamata a ɗora wa ƙasashe da hukumomi na yanzu alhakin laifukan da aka yi a tarihi ba.

Ƙudurin, wanda kamfanin dillancin labaran Reuters ya gani, yana kira ga ƙasashe su tattauna batun biyan diyya da kuma neman afuwa tare da mayar ababen tarihin da aka sace da kuma ba da diyya na kuɗi da alƙawarin cewa ba za a sake yin hakan ba.

Ƙasashen ƙungiyar Tarayar Afirka (AU) da na yankin Karibiyan da ma ƙasashe irin su Brazil sun goyi bayan ƙudirin.

Ministan harkokin wajen Ghana Samuel Ablakwa ya ce Ƙungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun riga sun ce ba za su goyi bayan ƙudirin ba.

Jakadun Ƙungiyar Tarayyar Turai da na Amurka a MƊD ba su mayar da martani nan-take ba ga buƙatar neman tsokaci game da batun.