| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An gano gawawwaki 9 a Jihar Neja ta Nijeriya, kwanaki bayan ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su
Ana zargin ’yanbindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar.
An gano gawawwaki 9 a Jihar Neja ta Nijeriya, kwanaki bayan ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su
Ya ce bayan samun labarin lamarin a ranar Talata, an tura tawagar ’yansanda da jami’an soji zuwa wurin domin kwashe gawawwakin.

Rundunar ’yansandan Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya ta tabbatar da gano gawawwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, ana zargin ’yanbindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya a kan hanyar.

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a Minna a ranar Laraba.

Ya ce bayan samun labarin lamarin a ranar Talata, an tura tawagar ’yansanda da jami’an soji zuwa wurin domin kwashe gawawwakin.

Ya ƙara da cewa an ƙara tsaurara ayyukan bincike da share fagen tsaro a yankin domin tabbatar da cewa babu wata barazana ga tsaro.

Ya ce, “An tura tawagogin ’yansanda da sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru; an kwashe gawawwakin, yayin da aka ƙara tsaurara ayyukan share fagen tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.”

Masu AlakaTRT Afrika - ‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi

Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun ceto mutane 308 da aka sace a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja.

Daga cikin mutanen 308 da aka ceto, 163 an sace su ne daga ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, yayin da wasu 145 aka sace a wani hari na daban a Jihar Neja.

An ceto mutanen ne daga dajin Kainji Lake National Park da ke Ƙaramar Hukumar New Bussa ta Jihar Neja, yayin wani samame na haɗin gwiwa da aka gudanar bisa bayanan sirri.

Aikin ya haɗa da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa, Rundunar Sojin Nijeriya, Hukumar DSS da Rundunar ’Yansandan Nijeriya.

 

Rumbun Labarai
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu  kwamandojin ISWAP tara a Borno
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
Super Falcons da Indomitable Lionesses na gogayyar shiga Gasar Kofin Duniya
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
An saki alƙalin da aka yi garkuwa da shi a jihar Kebbin Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya
Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa  da mutane 31 a Borno
Remi Tinubu ta nemi Saudiyya ta tallafa wa ilimin almajirai a Nijeriya
Nijeriya ta lalata makamai guda 2,819 da ta kama a matakin dakile rashin tsaro