| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
Wata mummunar musayar wuta tsakanin wasu mahara da ke ɗauke da makamai da jami’an tsaron Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwar jami’ai 10 da mahara 17 a wani ƙauye a Masarautar Zuru a kan iyakar jihohin Kebbi da Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
Mahukuntan Nijeriya an kashe 'yansandan kasar 10 a jihar Kebbi a wani harin 'yan bindiga a ranar 10 ga Agusta.

Wata mummunar musayar wuta tsakanin wasu mahara da ke ɗauke da makamai da jami’an tsaron Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwar ‘yansanda 10 a yanki mai nisa da ke arewacin ƙasar, in ji rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi a ranar Talata.

Arangamar, wadda ta afku a ranar Litinin a yankin ƙaramar Hukumar Sakaba da ke Masarautar Zuru a jihar ta Kebbi, ta kuma janyo mutuwar fararen hula biyu da mahara 17, in ji kakakin ‘yansandan Jihar ta Kebbi Bashir Usman a wata sanarwa da ya fitar.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu kwamandojin ISWAP tara a Borno

Har yanzu ba a san su waye suka kai harin ba a yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin, in ji ‘yansanda.

Kakakin ‘yansandan ya ce maharan sun far wa ƙauyen Makuku ne a Masarautar Zuru da ke kan iyakar Kebbi da Zamfara da nufin kai wa mazauna garin hari, da kuma yiwuwar yin garkuwa da wasusnsu.

Usman ya ce nan da nan jami’an ‘yansandan kwantar da tarzoma suka isa yankin, inda suka yi mummunar musayar wuta da ‘yanta’addan.

Jami’in ‘yansadan ya ce an kashe 17 daga maharan, sannan da dama sun gudu da raunin bindiga.