Farashin gangar ɗanyen mai ya ɗara $100 yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ƙamari

Tashin gauron zabin da ɗanyen mai ya yi na faruwa ne yayin da fargaba game da katse jigilar mai a mashigin ruwan Hormuz ta zarce ɗaukin gaggawa na gangar mai miliyan 400 da mambobin hukumar makamashi ta duniya IEA suka kawo.

By
Ana sayar da ko wace gangar ɗanyen mai samfurin Brent kan $101 da mislain ƙarfe 02. 00 na dare agogon GMT. / Reuters

Farashin ko wace gangar ɗanyen mai ya ɗara $101 ranar Alhamis, duk da cewa hukumar makamashi ta duniya (IEA) ta yi shelar yarjejeniya tsakanin ƙasashe 32 mambobinta ta fitar da ganga miliyan 400 na mai daga ma’ajiyar mai ta gaggawa, kamar yadda kafar wata labarai ta Al Jazeera ta ruwaito.

Farashin ɗanyen mai na kasuwar Futures for Brent crude, a kasuwar duniya ya ɗaga da kusan kashi 20 cikin 100 yayin da labarin ya gaza rage fargaba game da yadda katse jigilar mai na tsawon lokaci ta mashigin ruwan Hormuz.


Ana sayar da gangar mai samfurin Brent kan kusan $101 da ƙarfe 02. 00 na dare a agogon GMT, inda farashin ya ƙaru da fiye da kashi 38 cikin 100 daga matakin da aka gani kafin a fara yaƙin da Amurka da Isra’ila ke ƙaddamarwa kan Iran.

Ƙasashe mambobin hukumar IEA sun amince su fitar da gangar mai miliyan 400 daga ma’ajiyar mansu ta musamman, wani matakin fitar da mai mafi girma da aka taɓa ɗauka a tarihi, domin kwantar da hankulan kasuwannin da yaƙin na Gabas ta Tsakiya ya gigita, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana ranar Laraba.