Iran ba za ta amince da bukatu barkatai ba - Shugaba Pezeshkian

Ya ce a shirye Iran take ta bayar da dama don “a tantance” shirinta na Nukiliya kuma ya jaddada cewa kasar ba ta da shirin kera makamin Nukiliya.

By
Pezeshkian / AA

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ba za ta “amince da bukatu barkatai ba” dangane da shirin Nukiliyarta ba, bayan kasarsa ta dawo da tattaunawa da Amurka kan batun.

Ya ce a shirye Iran take ta bayar da dama don “a tantance” shirinta na Nukiliya kuma ya jaddada cewa kasar ba ta da shirin kera makamin Nukiliya.

Iran da Amurka sun dawo tattaunawa a makon jiya a karon farko tun bayan yakin da Iran da Isra’ila suka gwabza a watan Yunin da ya gabata, inda Amurka ta kai hari kan cibiyoyin Nukiliyar Iran.

“Iran ba za ta mika wuya ga masu tsangwamar ta ba, amma za mu ci gaba da tattaunawa da suka karfinmu da makwabtanmu don tabbatar da zaman lafiya a yankin,” in ji Shugaba Pezeshkian.

Shugaban Iran din yana magana ne a dandalin Azadi Square da ke babban birnin kasar Tehran, don yin bikin cika shekara 47 da yin juyin juya hali a kasar Iran.

“Kasarmu Iran, ba za ta yarda bukatu barkatai ba,” in ji shi.

Iran tana so tattaunawar ta mayar da hankali kan batun shirin Nukiliya, yayin da Amurka take son Iran ta dakatar da shirinta na makamai masu linzami da kuma daina nuna goyon baya ga wasu kungiyoyi da ke yankin.

Iran ta jaddada cewa shirin Nukiliyarta na zaman lafiya ne, ko da yake Amurka da kawarta Isra’ila sun yi amannar cewa tana shirin kera makamin Nukuliya ne.

Duk shekara magoya bayan gwamnatin Iran suna shirya gangami na murnar zagayowar kifar da gwamnatin Shah a shekarar 1979 wanda Amurka take goyawa baya.

A dandalin Azadi Square a ranar Laraba, wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya ga jami’an tsaro masu yawa fiye da wadanda aka gani a bara.

Iran ta yi fama da jerin zanga-zanga a watan jiya inda hukumomi suka mayar da martani da murkushe masu zanga-zangar, yayin da Amurka ta goya wa masu zanga-zangar baya da yin barazanar daukar matakin soja.