Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kashe ɓarayin daji 11 a Sokoto

Wasu rahotanni dai a Nijeriya suna cewa an kashe wani na hanun daman ƙasurgumin ɗanbindigar nan, Bello Turji, wato Kachalla Kallamu a kwanton-ɓaunan da sojoji suka yi wa ‘yanbindigar.

By
Sanarwar sojin ta ce dakarun Nijeriya sun ƙwace bindigogi ƙirar AK47 daga hannun 'yan ta'addan / AFP

Rundunar ta takwas ta sojin Nijeriya ta ce dakaru na musamman na Operation Fansan Yamma da aka tura daƙile aika-aikar ‘yan fashin daji da ta’addanci a jihar Sokoto sun yi wa ɓarayin daji wani  kwanton-ɓauna inda suka kashe 11 tare da ƙwace tarin makamai.

Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta wallafa a shafinta na X ta ce dakarun sun cim ma wannan ne ta hanyar wani farmaƙi na jarumta da dabara a ƙauyen Kurawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni inda suka daƙile wani hari da ‘yanbindigar suka yi shirin kaiwa a ƙauyen Tara.

Sanarwar ta ce dakarun sun yi aiki ne da bayanan sirri wajen aiwatar da kwanton-ɓaunar inda suka yi bata-kashi da ‘yanbindigar kafin su ci ƙarfinsu.

“Aikin ya sa an halaka 11 daga cikin ɓarayin dajin, yayin da saura suka tsere da raunuka a jikinsu,” in ji sanarwar.

 Dakarun sun ƙwace bindigogi ƙirar AK47 guda takwas da kuttun harsasai biyar da kuma harsasai 26,” a cewar rundunar.

Wasu rahotanni dai a Nijeriya suna cewa an kashe wani na hanun daman ƙasurgumin ɗanbindigar nan, Bello Turji, wato Kachalla Kallamu a kwanton-ɓaunar da sojoji suka yi wa ‘yanbindigar.

Sai dai ita sanarwar da rundunar sojin suka fitar ba ta tabbatara da wannan labarin ba.

Bello Turji dai yana cikin ‘yanbindigar da suka addabi mutane a yankin arewa maso yammacin Nijeriya inda suke garkuwa da mutane da kuma hase mutane da kuma kai hare-hare kan fararen hula.