| hausa
AFIRKA
3 MINTI KARATU
Sojojin Nijeriya sun kashe ɗan Bello Turji
Bello Turji yana cikin ɓarayin daji da suka yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane da kisa a arewa maso yammacin Nijeriya.
Sojojin Nijeriya sun kashe ɗan Bello Turji
Bello Turji ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa, in ji hedkwatar tsaron Nijeriya./Hoto:Hedkwatar Tsaron Nijeriya
20 Janairu 2025

Sojojin Nijeriya sun tabbatar da kashe wasu makusantan Bello Turji ɗaya daga cikin ɓarayin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Nijeriya.

Wata sanarwar da daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar ta ce samamen da sojin ƙasar suka kai Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da kuma Chindo sun yi sanadiyyar kashe gomman ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji da aka kashe a Fakai.

“Ƙarfin wutar da sojojin suka buɗe ya janyo mutuwar ‘yan ta’adda da yawa tare da lalata cibiyar adana kayayyakinsu. Harin ya kuma yi sanadiyyar ‘yanta wasu mutane da Bello Turji ya yi garkuwa da su. Kuma shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji, ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa,” in ji sanarwar.

Bello Turji yana cikin ɓarayin daji da suka yi ƙaurin-suna wajen garkuwa da mutane da kisa a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sai dai a ƙarshen shekarar da ta gabata dai hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kashe Bello Turji.

Kuma a ƙarshen makon jiya ne rahotanni suka ce ɗan ta’addan yana tsere wa harin sojojin Nijeriya.

Kazalika sojin ƙasar sun lalata dabar wani ɗan ta’adda da ake kira Idi Malam a kan hanyar dajin Zango Kagara, in ji sanarwar.

“A lokacin arangamar, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da kama mutum uku da ake zargi da haɗa baki da su,” in ji Janar Buba.

Baya ga haka sanarwa ta ce dakarun Nijeriyar sun kwace bindigogi iri-iri da kuma harsasai da alburusai da kuma shanu 61 da tumaki 44 da aka sace.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan