An buɗe sararin samaniyar Iran bayan rufe shi na wucin-gadi

An dawo da kai komon jiragen sama a sararin samaniyar Iran bayan karewar wa’adin takaita hakan, a yayinda jirage suka dawo shawagi a sararin samaniyar Iran a tsaka da rikicin yanki da na kasa da kasa.

By
Iran ta rufe sararin smaaniyarta na wucin gadi ga mafi yawan jirage in banda wasu da aka baiwa izini na zirga-zirgar kasa da kasa.

An sake buɗe sararin samaniyar Iran domin yin zirga-zirga bayan wa’adin rufe shi ga mafi yawan jiragen sama na ɗan lokaci ya ƙare, inda bayanai suka nuna jiragen sama suna kan hanyarsu ta zuwa Tehran.

FlightRadar24, wata cibiyar sa ido kan jiragen sama ta intanet, ta tabbatar a ranar Alhamis cewa sanarwar da aka bayar ga Ayyukan Jiragen Sama (NOTAM) da ta takaita amfani da sararin samaniyar Iran ta ƙare, kuma an ga jiragen sama da yawa suna shiga sararin samaniyar ƙasar.

Iran ta rufe sararin samaniyarta na ɗan lokaci ga duk jiragen sama ban da masu shigowa da tashi daga ƙasashen waje da aka ba izini, tana ambaton dalilai na tsaro bisa daukar matakin.

Sanarwar farko ta bayyana cewa sararin samaniyar Tehran zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar 15 ga Janairu, wanda hakan ya ba da dama ga jiragen sama na farar-hula na musamman su yi aiki tare da amincewar Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Farar-hula.

Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin da kuma cikin gida, ciki har da zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran da kuma ƙaruwar sanya idanun ƙasashen duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an sanar da shi cewa an dakatar da aiwatar da hukuncin kisa ga masu zanga-zanga a Iran, yayin da yake gargaɗin cewa Washington za ta sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa.

Trump ya sha bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zanga kuma ya ce Amurka za ta iya ɗaukar "mataki mai ƙarfi" idan aka aiwatar da hukuncin kisan.

Ministocin Harkokin Waje na G7 sun kuma yi Allah wadai da "yin amfani da ƙarfin tuwo da gangan" kan masu zanga-zanga, suna kira ga hukumomi da su nuna kamun kai da girmama hakkin ɗan’adam, yayin da suke gargaɗin yiwuwar ɗaukar ƙarin matakai.

A halin yanzu, jami'an Iran sun zargi Amurka da Isra'ila da goyon bayan tashin hankali da ta'addanci da ke da alaƙa da zanga-zangar - iƙirarin da ƙasashen yamma suka musanta.

Hukumomin Iran ba su fitar da alƙaluman waɗanda suka mutu a hukumance ba, yayin da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam suka bayar da rahoton cewa dubban mutane sun mutu tare da jikkata tun lokacin da zanga-zangar ta fara a ƙarshen watan Disamba.