| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Shugaban Rundunar Sojin Iran ya yi barazanar mayar da martani ga Trump da Netanyahu
Zan-zangar matsin tattalin arziki a Iran ta janyo hankulan kasashen duniya, ciki har da shugabannin kasashe abokan hamayya, Isra’ila da Amurka, wanda ya tilasta wa sojoji mayar da martani.
Shugaban Rundunar Sojin Iran ya yi barazanar mayar da martani ga Trump da Netanyahu
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta zargi Trump da Netanyahu da tayar da hankali da kuma kokarin kawo cikas ga hadin kan kasar Iran. / Reuters
7 Janairu 2026

Babban hafsan sojin Iran ya yi gargadin cewa kasar ba za ta tsaya ta tana kallo a yi mata barazana daga ƙasashen waje ba, bayan da Amurka da Isra'ila suka goyi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.

"Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ɗauki ƙaruwar kalaman batanci ga al'ummar Iran a matsayin barazana kuma ba za ta lamunci ci gaba da hakan ba tare da mayar da martani ba," in ji Janar Amir Hatami, a cewar kamfanin dillancin labarai na Fars.

Hatami, kwamandan sojojin Iran ya yi gargaɗin cewa "idan maƙiya suka yi kuskure," martanin Iran zai fi ƙarfi fiye da lokacin yaƙin kwanaki 12 da Isra'ila na watan Yunin da ya gabata.

A cikin 'yan kwanakin nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shiga tsakani a Iran idan aka kashe masu zanga-zanga, yayin da Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya nuna goyon baya ga zanga-zangar.

A ranar 28 ga Disamba, 'yan kasuwa a Tehran sun gudanar da zanga-zanga kan hauhawar farashi da rugujewar kudin kasar rial, wanda ya haifar da daukar irin wannan mataki a birane da dama.

Zanga-zangar ba ta kai matsayin zanga-zangar 2022 zuwa 2023 ba, ballantana zanga-zangar da aka yi a titunan kasar a shekarar 2009 bayan zaben shugaban kasa.

Masu AlakaTRT Afrika - Shin Amurka ta yi nasarar lalata ƙarfin nukiliya na Iran?

Amma zanga-zangar tattalin arziki ta jawo hankalin kasashen duniya, ciki har da shugabannin kasashen da ke adawa da Iran.

"Muna kallon ta sosai. Idan suka fara kashe mutane kamar yadda suka yi a baya, ina ganin Amurka za ta far musu da karfi," in ji Trump ga manema labarai a ranar Lahadi.

A halin yanzu, Netanyahu ya shaida wa majalisar ministocin Isra'ila cewa "Muna goyon bayan gwagwarmayar al'umar Iran da kuma burinsu na samun 'yanci da adalci."

A ranar Litinin, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta zargi Trump da Netanyahu da tayar da hankali da kuma kokarin kawo cikas ga hadin kan kasar Iran.

Yakin da aka yi a watan Yuni ya fara ne da harin da Isra'ila ta kai wa sojojin Iran da cibiyoyin nukiliyarta.

Amurka ta shiga cikin hare-haren na dan lokaci, inda ta kai hari kan manyan wuraren nukiliya na Iran guda uku.

Rumbun Labarai
Abin da ya sa ya kamata Afirka ta damu kan samamen da Amurka ta kai Venezuela
An sayar da kifi mai nauyin kilogiram 240 a kan Naira biliyan 4.5 ($3.2m) a Japan
Me zai faru ga takunkuman da Amurka ta sanya wa Venezuela bayan ta ɗauke Maduro
Tarayyar Afirka ta nuna 'damuwa', Afirka ta Kudu ta nemi a yi taron MDD da gaggawa kan Venezuela
Trump ya gargaɗi Colombia, ya nufi Cuba bayan ya kama Maduro
Amurka ba za ta bari kowa ya ci gaba daga inda Maduro ya tsaya ba - Trump
Martanin duniya na karuwa kan hare-haren da Amurka ta kai wa Venezuela
An fitar da Shugaba Maduro da matarsa daga Venezuela, in ji Trump
Ƙarar bamabamai ta rikita birnin Caracas bayan Trump ya sha alwashin kai hari a ƙasar Venezuela
Zanga-zangar Iran kan matsin tattalin arziki ta rikiɗe zuwa tashin hankali
Hotuna: Wasan tartsatsin wuta da sauran bukukuwa na maraba da Sabuwar Shekara ta 2026
Fiye da mutum 3,000 ne suka mutu a tafiya ci-rani Turai ta Spain a 2025: Rahoto
Somalia ta yi watsi da amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland a matsayin barazana ga yankin
Turkiyya ta yi tir da Israila kan amincewa da Somaliland
Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma
Rasha na shirin gina tashar nukiliya a duniyar wata nan da shekaru 10 masu zuwa
Babban hafsan sojin Libya da jami'ai sun mutu a hatsarin jirgin sama a kusa da Ankara: Dbeibah
Trump ya saka ƙasashen Afirka biyar cikin jerin da ya haramta wa shiga Amurka
Garin da yake shafe kwana 66 a cikin dare babu hasken rana
An kashe sojojin Bangladesh da ke aikin wanzar da zaman lafiya a sansanin MDD na Sudan: Bangladesh