| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya na nuna kayan tsaro da ta ƙera a taron baje-kolin SAHA 2026 da ke gudana a Istanbul
Karamin Ministan Tsaro na Nijeriya Bello Matawalle ne ya jagoranci tawagar kasar zuwa birnin Istanbul na Turkiyya don halartar baje-kolin kayan tsaro na kasa da kasa na SAHA 2026.
Nijeriya na nuna kayan tsaro da ta ƙera a taron baje-kolin SAHA 2026 da ke gudana a Istanbul
Karamin Ministan Tsaro na Nijeriya a wajen baje-kolin kayan tsaro na kasa da kasa SAHA 2026 da ke gudana a Istanbul, Turkiyya / Hoto: TRT Afrika Hausa / TRT Afrika Hausa

Nijeriya na cikin jerin kasashen duniya da ke nuna kayan tsaron da ƙasar ta samar, a wajen taron baje-kolin kasa da kasa na SAHA 2026 da ke gudana a birnin Istanbul na Turkiyya.

A zantawarsa da TRT Afrika Hausa, Ƙaramin Ministan Tsaro ya ce an kafa tarihi yadda aka baje-kolin bindigogi ƙirar Nijeriya, wanda ba a taba samun irin haka a kasar ba.

Ya ce Nijeriya na halartar bajekolin don ita ma a dama da ita, ta nuna wa duniya irin tata fasahar ga duniya.

“Za ka ga kasashe na zuwa na duba wannan waje domin ganin cewa su ma ya za su zo su sayi wadannan kayayyaki da muke yi a Nijeriya,” in ji Matawalle.

Masu AlakaTRT Afrika - An fara baje-kolin kayan tsaro da sufurin sararin samaniya na SAHA 2026 a Istanbul

Ya ce wannan shi ne karo na farko da za ka ga Nijeriya ta samu wakilci a irin wadannan wurare na tarukan kasa da kasa, inda a yanzu ta samu damar nuna wa duniya fasaharta.

Kofar Nijeriya a bude take don kawo cigaba da samar da tsaro

Karamin Ministan Tsaron na Nijeriya ya kuma ce sakamakon irin kyawawan manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kasar ta janyo hankulan masu sha’awar kawo cigaba da samar da tsaro.

Ya ce manufarsu a nan ita ce ganin Nijeriya ta tsaya da kafarta wajen samar da kayan tsaro, ta yadda ba sai ta je wata kasar tana sayen kayayyakin ba don kawo karshen matsalolin tsaro.

Matawalle ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu bisa ba shi damar farfado da wannan ma’aikata wadda a yanzu har tana halartar baje-kolin kayan tsaro a duniya.

Ya kara da cewa Nijeriya da Turkiyya sun kulla yarjejeniyar yadda ‘yan kasar Turkiyya za su je Nijeriya su samar da kayayyakin tsaro don amfanin kasar da sauran kasashen yankin.

Ya ce “A yanzu mun bayar da karfi kan komai sai dai a je Nijeriya a kera maimakon mu je waje mu saya.”

An fara taron baje-kolin kayan tsaro na kasa da kasa na SAHA 2026 a birnin Istanbul na Turkiyya, wanda za a kammala a ranar 9 ga Mayun 2026.