Hedkwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa fararen-hula sun mutu a wani harin sama da sojojin ƙasar suka kai a jihar Neja da ke arewacin ƙasar.
Hedkwatar tsaron ta ce sojojin sun kai hare-hare ta sama ne a wuraren da aka tabbatar cewa mafakar ‘yanbindiga ce a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ambato wata sanarwa da daraktan watsa labaran hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar ranar Lahadi tana cewa an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna haɗuwar ɓarayin daji a ƙauyen Lukupe na ƙaramar hukumar Shiroro ranar 9 ga watan Mayu na shekarar 2026.
Rundunar Sojin ta ce bayan wannan ne dakarun da ke aiki da jirage marasa matuƙa suka kai hare-haren sama tsakanin ƙarfe 11:59 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu a maɓoyar ‘yanbindiga a ƙauyukan Katerma da Bokko Kusasu da Kuduru.
Manjo Janar Onoja ya bayyana cewa majiyoyin bayanan sirri na yankin sun tabbatar da cewa hare-haren sun “sauka a wuraren da aka nufa” a ƙauyukan Kusasu da Katerma da kuma Bokko.
Ya ce ce kimanin ɓarayin daji 70 aka kashe a Kusasu kaɗai, yayin da aka ga mayaƙan da suka tsira sun ɗauki gawarwakin abokansu domin binne su.
Sanarwar ta ce, “Bisa aikin da aka bai wa rundunar sojin Nijeriya na aikata ayyuka na kakkaɓe duk wani nau’i na rashin tsaro a ƙasar, ranar 9 ga watan Mayu na shekarar 2026, bayanan sirri sun nuna taruwar ‘yanbindiga a ƙauyen Lukupe na ƙaramar hukumar Shiroro.
”Daga baya, a ranar 10 ga watan Mayu na shekarar 2026 tsakanin ƙarfe 11:59 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya, rundunar jirage marasa matuƙa ta sojojin Nijeriya yayin da take aiki bisa bayanan sirri ta kai hare-hare na sama kan maɓoyar ‘yanbindiga a ƙauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da kuma Kuduru a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
“Ƙarin rahotanni daga majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa hare-haren saman sun dira daidai kan wuraren da aka kai su a Kusasu da Katerma da kuma Bokko… An samu bayanan cewa kimanin ‘yanbindiga 70 ne hare-haren suka kashe a Kusasu. ”

Da yake mayar da martani ga rahotannin da ke iƙirarin cewa an kashe fararen-hula a lokacin samamen, Manjo Janar Onoja ya ce an kai hare-haren ne bisa bayanan sirri masu tushe da suka tabbatar da kasancewar ‘yanta’adda a wuraren.
Ya ƙara da cewa mazauna wuraren sun riga sun bar yankin zuwa Sarkin Pawa kafin a fara kai hare-hare.
“Hedkwatar Tsaro na son ta yi bayani bisa wasu rahotannin da ke yawo a wasu wurare da ke iƙirarin cewa an kashe fararen-hula a harin sama da aka kai da sanyin safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun shekarar 2026, a ƙauyukan Katerma da Bokko da Kusasu da kuma Kuduru a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
”An shirya aikin ne dalla-dalla kuma aka aiwatar da shi bisa bayanan sirri masu tushe lamarin da ke tabbatar da taruwar ‘yanta’adda a waɗannan wuraren.
“Saɓanin labarin da ake yaɗawa, hare-haren saman sun dira daidai kan wuraren da aka gano cewa maɓoyar ‘yanta’adda ne kuma sun cim ma manufofinsu na soji, inda suka kassara kimanin ‘yanbindiga saba’in a Kusasu kawai, ” in ji Onoja.
Hedkwatar tsaron ta ce binciken bayan hare-hare ya nuna cewa masu aikata aikata laifuka aka kashe ba fararen-hula ba.
Sai dai kuma, ya ce an tura dakarun da suka dace domin su duba sahihancin waɗannan zarge-zarge na mutuwar fararen hula.
Onoja ya yi kira ga kafofin watsa labarai da kuma jama’a su kauce wa yaɗa rahotannin da ba su da tushe da ke iya yin zagon ƙasa ga ayyukan soji.
“Rundunar sojin Nijeriya na nan a jajirce wajen kare dukkan ‘yan ƙasa masu biyayya ga doka kuma tana aiwatar da dukkan ayyukanta bisa dokokin aiki,” in ji Onoja.
Bayanin na hedkwatar tsaron Nijeriya ya biyo bayan rahotannin da suka yi ta yawo ne ranar Lahadi da ke zargin cewa an kashe wasu fararen-hula da ba a bayyana adadinsu ba yayin hare-haen sama a Guradnayi, wani ƙauye kusa da Kusasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.











