Rundunar sojin Nijeriya ta kashe ‘yan ta’adda 47 a farmaki da ta kai a faɗin ƙasar

A Jihar Sokoto, dakaru daga bataliyoyi a Kananan Hukumomin Binji da Tangaza sun kashe 'yan ta'addar Lakurawa uku a yayin samame na kwanton-ɓauna.

By
Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Nijeriya Waidi Shaibu ya ce suna ci gaba da kai farmaki tare da goyon bayan mutane da kyakkyawan aikin leƙen asiri / Nigerian army

Rundunar Sojin Nijeriya ta samu manyan nasarori a samamen da ta kai kan ‘yan ta’adda a faɗin ƙasar cikin awanni 72 da suka gabata, inda ta kashe gawurtattun 'yan ta'adda 47, a cewar wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Sanarwar, wadda rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ƙara da cewa dakatunta sun kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ceto mutane fiye da mutum 30 da aka yi garkuwa da su da ƙwato tarin makamai, harsasai da sauran kayan aiki na ɓata-gari.

Waɗannan jerin samame da aka tsara sannan aka kai su ta ƙasa da ta sama sun nuna ɗorewar jajircewar Sojojin Nijeriya wajen murƙushe 'yan ta'adda, 'yan fashi, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata muggan laifuka da ke barazana ga tsaron ƙasa, in ji sanarwar.

A yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sojoji sun kai samame ta ƙasa bayan samun sahihan bayanan sirri.

A Jihar Sokoto, dakaru daga bataliyoyi a Kananan Hukumomin Binji da Tangaza sun kashe 'yan ta'addar Lakurawa uku a yayin samame na kwanton-ɓauna, inda suka ƙwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, babur, rediyon sadarwa, wayoyin hannu da sauran kayayyaki.

An fatattaki ‘yan ta’adda a tsakiyar Nijeriya

Kazalika, a Jihar Neja, sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda a kan babura a karamar Hukumar Munya, inda suka kashe wani ɗan ta'adda tare da ƙwato makamai, harsasai, kayan sadarwa da kayan aiki.

A Jihar Zamfara, ci gaba da sintirin sojoji a Kananan Hukumomin Anka da Maru ya kawo cikas ga ayyukan ta'addanci, an kashe 'yan ta'adda biyu, an lalata maɓoyarsu, an kuma ceto fararen-hula da suka samu raunuka da dama.

Yayin da a Jihar Kaduna, ayyukan da sojoji suka gudanar a Kananan Hukumomin Sanga da Zangon Kataf sun daƙile yunƙurin fashi da makami da garkuwa da mutane tare da kuɓutar da waɗanda abin ya shafa sannan an kama wadanda ake zargi da satar shanu.

A yayin farmakin an ƙwato kayan aiki da suka hada da bindiga ƙirar gida, harsasai da kuma dabbobin da aka sace.

Kazalika an samu irin wannan nasara a Jihar Filato, inda sojoji suka kama mutane uku da ake zargi da satar shanu a Kananan Hukumomin Barikin Ladi da Wase, sun kuma ƙwato babura, wuƙaƙe, wayoyin hannu da kuɗi.

Babbar nasara a yankin kudu maso kudu

A farmakin da aka kai a yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas an samu sakamako mai kyau, in ji rundunar sojin ta Nijeriya.

A Jihar Ribas, sojoji sun daƙile ayyukan da aka shirya ba bisa doka ba a kan hanyar Cawthorne a Karamar Hukumar Degema, inda suka kama mutane biyu da ake zargi da kuma ƙwato kayan aiki da aka yi niyyar amfani da su don yin ɓarna.

A Jihar Delta, sojoji sun gano jiragen ruwa biyu na katako da ke ɗauke da kimanin lita 1,700 na man fetur da aka sace, wanda hakan na yin illa ga tattalin arzikin Nijeriya.

A Jihar Imo, an kama wani da ake zargi da hannu a harbin wani farar-hula kuma aka miƙa shi ga 'yansandan Nijeriya don ci gaba da bincike.

A Babban Birnin Tarayya, a farmakin yaƙi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba an samu nasarar kama wasu da ake zargi su 11 tare da ƙwace babur da man fetur.

Ana ci gaba da farmaki ta sama a arewa maso-gabas

A halin yanzu, Rundunar Sojin Sama ta ci gaba da kai farmaki a wuraren 'yan ta'adda a Arewa maso-gabas.

Farmakai ta sama da aka yi nasarar kai wa sun nufi sansanonin jigilar kayayyaki na ‘yan ta’addar ISWAP/JAS da wuraren haɗuwarsu da ke Jihar Borno .

Jami’an tsaron sun kashe aƙalla 'yan ta'adda 42, inda fashewar wasu abubuwa ya kai ga lalata tarin makamai da abubuwan fashewa.

Farmakin ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'adda, wanda hakan ya ƙara kassara ƙarfin ikonsu.

A wurare daban-daban, sojojin Nijeriya sun ceto fiye da mutane 30 da aka sace, ciki har da mata da yara.

An kwashe waɗanda abin ya shafa lafiya, an kuma ba su kulawar da suke buƙata tare da mika su ga iyalansu.

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana ƙwato bindigogin samfurin AK-47, mujallu, harsasai, rediyon sadarwa, babura, wayoyin hannu da sauran kayan aiki masu mahimmanci ga aikata munanan laifuka.

Muhimmancin bai wa jami’an tsaro hadin kai

Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Laftanal Janar Waidi Shaibu ya jaddada cewa suna ci gaba da kai farmaki tare da goyon bayan mutane da kyakkyawan aikin leƙen asiri da tabbatar da kare rayukan fararen-hula.

Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar wa jama'a alƙawarinta na ci gaba da kai farmaki da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro sai an samu zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin ƙasar.