Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun kashe ‘yan ta’adda na ƙungiyar ISWAP da masu garkuwa da mutane da dama a hare-haren daƙile ta’addanci da fashin daji da suka kai a arewacin ƙasar.
Lamarin ya faru ne sakamakon jerin hare-haren sama jiragen yaƙin suka kai inda suka kashe ‘yan ta’adda a Mallam Fatori da Shuwaram a Jihar Borno tare da lalata mafakar ɓarayin daji a Garin Dandi da Chigogo da ke Jihar Kwara da kuma dutsen Zango a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar, ta ce aikin na haɗin gwiwa da aka yi ranar 9 ga watan Nuwambar shekarar 2025 wata manuniya ce ga mahimmim mataki na yaƙin da dakarun Hadin Kai da Operation Fansan Yamma ke yi na ganin sun daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da ƙungiyoyi masu aikata laifuka a arewacin ƙasar.
“A jihar Borno, hare-haren saman sojin saman Nijeriya sun yi kaca-kaca da ‘yan ta’addan ISWAP da suka kafu a arewacin Tumbuns.

“Bayan samu bayanan sirri da kuma yin bincike, jiragen yaƙi sun ƙaddamar da hare-haren sama a kudu maso gabashin Shuwaram da Mallam Fatori, inda aka ga ‘yan ISWAP suna taruwa da babura da kwalekwale kusa da Tafkin Chadi.
“Hare-haren sun lalata mafakar masu tayar da ƙayar bayan da wuraren ajiye ababen hawa da makamai inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama tare da katse hanzarinsu. Binciken da aka yi bayan hari ya tabbatar da kashe ‘yan tadda da kuma rage ƙarfin ISWAP a yankin,” in ji sanarwar.
Hare-haren Kwara
Hedkwatar rundunar sojin saman ta bayyana cewa jiragen samanta sun kai hare-hare a lokaci ɗaya a Garin Dandi da Chigogo a Jihar Kwara, inda suka afka wa sansanonin ɓarayin daji kai-tsaye bisa bayanan sirri.
“Hare-haren sun haddasa asara da yawa kan masu aikata laifukan,” in ji sanarwar.
Ta ƙara bayyana cewa a wani aiki mai kama da hakan, jiragen yaƙin a ƙarƙashin aikin Operation Fansan Yamma sun kai hari a Dutsin Zango a Kankara, da ke Jihar Katsina, mafakar wani babban ɗan ta’adda da mayaƙansa.
“Bisa samun bayanan sirri da kuma bincike, an ƙaddamar da hare-hare inda aka lalata muhimman wuraren sufuri da kuma kashe wasu daga cikin ‘yan ta’adda a ɗaya daga hare-haren da suka fi ƙarfi a yankin.
“Rundunar Fansan Yamma ta ƙaddamar da aikin tattara bayanai ta sama a arewa maso yammaci da ya ƙunshi muhimman garuruwa a jihohin Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, ciki har da Kakihum da Dankolo da Kotonkoro da kuma Kuyello.
“Waɗannan wuraren sanannun hanyoyi da mafaka ne ga ƙungiyoyi na ‘yan bindiga a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua. A lokacin aikin wanda aka yi da haɗin gwiwar sansanonin soji a Dankolo da Kotonkoro ya nuna wani motsi mai cike da tuhuma kusa da Dutsen Wam, inda aka ga ‘yan ta’adda kan babura suna ƙoƙarin tserewa.
“Nan-take jami’an da ke tuƙa jiragen saman suka kashe ‘yan ta’addan kuma ba a ga wani motsin ‘yan ta’adda ba,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin saman ta ce nasarar aikin mara kuskure a jihohin Borno da Kwara da Katsina da yankin arewa maso yammacin ƙasar ta nuna sabunta matsa ƙaimi wajen daƙile ta’addanci bayan umarnin babban hafsan sojin saman ƙasar, Air Marshal Sunday Aneke.


















