Turkiyya na shirya tsarin tsaron Patriot domin kare sararin samaniyarta yayin yaƙin Iran

Ma'aikatar tsaro ta ce dakarun Turkiyya suna aiki da NATO domin ƙarfafa tsare-tsaren tsaron sararin samaniya a matsayin martani ga yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran.

By
Dakarun Turkiyya suna tsara ayyukan Patriot da ƙawayen NATO . [Tshohon oto] / AA / AA

Turkiyya ta ce ana shirya wani tsarin tsaron sararin samaniya na Patriot domin ya fara aiki a gabashin ƙasar a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake tare da NATO domin kare sararin samaniyar ƙasar yayin tashe-tashen hankulan da ake yi a yankin.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, ma’aikatar tsaron ta ce rundunar sojin Turkiyya tana nan a “jajirce domin tabbatar da tsaron ƙasarmu da ‘yan ƙasarmu ” game da abubuwan da ke faruwa a yankinmu a baya bayan nan.

“Duba da abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan a yankinmu, ana ɗaukar matakai da suka kamata domin kare kan iyakokinmu da sararin samaniyarmu kuma muna tattaunawa da ƙawancen NATO da ƙawayenmu,” in ji ma’aikatar.

Ta ƙara da cewa, tare da matakan tsaron ƙasa, ƙawancen ta ƙara ƙarfafa matakan kare kanta a yankin.

“Baya ga matakai na ƙasa da muka ƙaddamar, NATO ta ƙarfafa mataken kare sararin samaniyar da na kariya daga makamai masu linzami,” in ji sanarwar.

“Baya ga wannan tsarin, akwai wani tsarin tsaron sararin samaniya na Patriot da ke Malatya kuma ana shirya shi domin ya fara aiki domin kare sararin samaniyarmu,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.

Malatya na ɗauke da wata tashar na’urar ba da gargaɗi da wuri, wadda ƙawancen NATO ya kafa a shekarar 2012, domin hango makamai masu linzami.

Tsare-tsaren kare sararin samaniya na NATO sun kakkaɓo ƙarin wani makami mai linzami da aka harbo daga Iran wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya ranar Litinin, wanda ya zama karo na biyu na samun irin wannan lamari na shigar makamai masu linzami na Iran sararin samaniyar Turkiyya a makon da ya gabata.

Ankara na tabbatar da tsaro a mataki mafi a’ala

Ma’aikatar ta ce Turkiyya za ta ci gaba da aiki tare da ƙawancen game da lamuran da suka shafi tsaron ƙasa da tsaro.

“Ƙasarmu, wadda ke ci gaba da aiwatar da ikon tsaron ƙasa da tsaro a mataki mafi ƙarfi, za ta ci gaba da nazari kan abubuwan da ke faruwa a wani yanayi na haɗin gwiwa da tuntuɓar juna da ƙawancen NATO da ƙawayenmu, da kuma ƙoƙari wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali na yanki,” in ji sanarwar.

Sanarwar na zuwa ne yayin tashe-tashen hankula na yanki sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila ke ƙaddamarwa kan Iran .

Tashe-tashen hankulan sun yi ƙamari tun lokacin da Isra’ila da Amurka suka ƙaddamar da hare-haren hadin gwiwa kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya kashe kimanin mutum 1,300 kawo yanzu, ciki har da jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei.

Iran ta ɗauki fansa da hare-haren jirage mara matuƙa da makamai masu linzami kan Isra’ila da Jordan da Iraq da kuma wasu ƙasashen Larabawa da ke karɓar baƙuncin kayayyakin sojin Amurka .

Iran ta kuma ce ta rufe mashigin ruwan Hormuz a ranar 1 ga watan Maris .

Muhimmiyar hanyar ta ruwa dai a lokacin da babu matsala tana samun shigewar gangar mai miliyan 20 a ko wace rana da kuma kimanin kashi 20 cikin 100 na iskar gas da ake amfani da shi a duniya

.