| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
A cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar 'Yansandan Jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce aikin da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri ya kai ga nasarar ƙwato babura 17, kekuna uku, janareta guda ɗaya, lasifikoki uku da ganguna uku.
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi fama da hare-haren 'yanbindiga

Rundunar 'Yansandan Jihar Zamfara, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ta kama mutane 48 da ake zargi yayin wani samame da suka kai a maɓoyar masu laifi a cikin birnin Gusau.

A cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar 'Yansandan Jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce aikin da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri ya kai ga nasarar ƙwato babura 17, kekuna uku, janareta guda ɗaya, lasifikoki uku da ganguna uku, waɗanda ake zargin masu aikata laifuka ne suka bari.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama, kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Masu AlakaTRT Afrika - 'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya

Sanarwar ta ce Kwamishinan 'Yansandan Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya sake jaddada aniyar rundunar ta ci gaba da yaƙi da aikata laifuka da kuma tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin jihar.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi fama da hare-haren 'yanbindiga, inda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke yawan sace mutane domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da kuma kai hare-hare kan al'ummomin karkara.

A watannin baya-bayan nan, jami'an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da hare-hare domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya a jihar.