Trump ya fi son diflomasiyya da Iran, amma ya lashi takobin hana Tehran mallakar nukiliya
A jawabinsa na farko na Halin Da ƙasa ke Ciki a wa'adin mulkinsa na biyu, Shugaba Trump ya bayyana son bin tafarkin diflomasiyya wajen warware rikicin nukiliyar Iran.
Shugaba Donald Trump ya yi amfani da jawabinsa na Halin Da Ƙasa Ke Ciki don nuna son bin hanyar diflomasiyya da Iran, duk da cewa yana da ra’ayin riƙau kan burin Tehran na mallakar makamin nukiliyar.
Da yake magana ga wani zama na haɗakar ‘yan majalisar dokokin ƙasar ranar Talata, Trump ya tabbatar da cewa Amurka tana tattaunawa da Tehran.
"Muna tattaunawa da Iran, kuma suna son su cim ma yarjejeniya," kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar.
Ya jaddada cewa duk da cewa shi ya fi son bin hanyar diflomasiyya, gwamnatinsa ta jajirce kan manufar da Amurka ta daɗe a kai ta neman ganin Tehran ba ta samu ƙarfin nukiliya ba.
"Ba zan taɓa ƙyale ƙasar da ta fi ɗaukar nauyin ta’addanci a duniya ta mallaki makamin nukiliya ba," kamar yadda Shugaba Trump ya sha alwashi.
Duk da maganar diflomasiyya, Trump ya yi amfani da jawabin wajen bayyana ruɗanin cikin gida a cikin Iran, yana mai iƙirarin cewa “gwamnatin ƙasar ta kashe masu zanga-zanga 32,000” a lokacin rikicin da aka yi kwanan baya.
Ya bayyana dabarar “matsin lamba mafi tsanani” na gwamnatinsa a matsayin abin da ya sa Tehran ta koma teburin tattaunawa, yana mai iƙirarin cewa Amurka tana tattaunawa daga wani mataki na ƙarfi da ba a taɓa samu ba.
"Cikin gomman shekaru, manufar Amurka ta dogara ne a kan hana Iran mallakar makamin nukiliya," in ji Trump .
Ya bayyana cewa duk da cewa zaɓin ɗaukar matakin soji na nan a kan teburi, "mafita ta diflomasiyya" ita ce mafitar da aka fi so domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma tsaron ƙasa.