Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa

Ƙungiyar Amnesty ta yi zargin cewa ana tsarewa da kuma barazana da tsoratar da masu sukar gwamnatin jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba bisa ƙa’ida ba saboda bayyana ra’ayoyinsu.

By
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta soki yadda gwamnatin jihar Kano ta musgunawa 'yan adawa

Kungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Amnesty International ta soki gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya game da matakin da take ɗauka na ci gaba da musguna wa ‘yan adawa.

A wata sanarwa da Amnesty ta fitar ranar Alhamis, ta ce jami’an tsaro suna yawan kamawa ko kuma gayyatar mutane, musamman waɗanda ke wallafa kalamai masu sukar gwamnatin Kano a kafafen sada zumunta.

Kazalika, ƙungiyar ta yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama an gurfanar da su a gaban kotu cikin gaggawa bisa zarge-zargen da ta bayyana a matsayin marasa tushe, sannan aka yanke musu hukunci cikin hanzari.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa ana tsarewa da kuma barazana da tsoratar da masu sukar gwamnatin jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda bayyana ra’ayoyinsu.

Amnesty ta ba da misali da wani Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass, na wanda ta ce “yana ci gaba da kasancewa a tsare tun watan Agusta.”

Ta ƙara da cewa akwai wani mai suna Alhaji Murtala Muhammad Dawanau wanda ke cikin waɗanda aka tsare da su ba bisa ƙa’ida ba saboda wani tsokaci da ya yi a wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook.

Kungiyar ta ce an kuma kama Fatima Dayyabu, wadda aka gurfanar da ita gaban kotu tare da cin tarar ta saboda sukar gwamnati.

Sauran mutanen da Amnesty ta ambata sun haɗa da Maryam Usman, wadda aka fi sani da Golden Queen da Muhammad Ahmad da Hafsat Muhammad Sauwama Kauwama da Khadija Garba Kadnass da Ismail Hassan Hussain Lajin Dala da kuma Isa Zanna Isa.

Sanarwar Amnesty ta kuma ce har yanzu wani Zaidu Magaji yana fuskantar abin da ta kira barazana da tsoratarwa.

Amnesty ta ce waɗannan kame-kame da kuma zargin musgunawar an fi yi wa ‘yan siyasa masu adawa da magoya bayansu, tana mai gargadin cewa lamarin na haifar da yanayin tsoro a jihar Kano.

Kungiyar ta jaddada cewa sukar zaɓaɓɓbun shugabanni na daga cikin ‘yancin faɗar albarkacin baki, tare da kira ga gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro da su mutunta ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta sha musanta irin waɗannan zarge-zarge daga Amnesty International, tana mai cewa wasu daga cikin matakan jami’an tsaro na da nasaba da ƙorafe-ƙorafe da zarge-zargen aikata laifuka, ciki har da cin zarafi ta kafar intanet, da ɓata suna da kuma tunzura jama’a.

Zarge-zargen na baya bayan nan sun sake haifar da muhawara a Nijeriya kan yadda za a daidaita ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma aiwatar da dokokin da suka shafi kalaman da ake wallafawa a shafukan intanet da sukar jami’an gwamnati.